Lokaci Ya Yi: Malamin Jami'ar UniUyo da Aka 'Zalunta' Tsawon Shekara 24 Ya Rasu

Lokaci Ya Yi: Malamin Jami'ar UniUyo da Aka 'Zalunta' Tsawon Shekara 24 Ya Rasu

  • Malamin jami'ar UniUyo wanda aka kora ba bisa ƙa'ida ba na tsawon shekaru 24, Dr. Inih Ebong ya riga mu gidan gaskiya
  • Matarsa, Uduak Ebong ce ta sanar da rasuwarsa ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu, 2025 a asibitin koyarwa na Jami'ar Uyo
  • Ya sha fama da ciwon zuciya ga talauci saboda rasa aikinsa da ya yi amma daga bisani Femi Otedola ya ɗauki ɗawainiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Dr. Inih Ebong, tsohon malamin jami'ar Uyo (UniUyo) a bangaren koyar da wasan kwaikwayo, wanda aka sallama daga aiki ba bisa ƙa'ida ba, ya mutu.

An ruwaito cewa Jami’ar Uyo ta kori malamin ba bisa ka’ida ba shekaru 24 da suka gabata.

Dr. Ebong.
Malamin Jami'ar UniOyo da aka zalunta ya riga mu gidan gaskiya Hoto: Dr. Inih Ebong
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa Dr. Ebong ya rasu yana da shekaru 73 a duniya bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan

"Sai yanzu ka san yana da kima?" El Rufa'i ya tunawa Ganduje ya kira Buhari Habu na Habu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon malami a Jami'ar UniUyo ya rasu

Matarsa, Uduak Ebong, ta tabbatar da rasuwar mijinta da safiyar Laraba, 16 ga Afrilu 2025, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Uyo, inda ya ke kwance.

Ta ce “Ya rasu,” cikin murya mai rawa, tana bayyana cewa mijinta yana ta magana a gadon asibiti da daddare, amma da ta farka da safe sai ta tarar da shi babu rai.

Dr. Ebong ya sha fama da matsin rayuwa tun bayan da jami’ar ta sallame shi a shekarar 2002, saboda sukar da ya ke yi wa shugabannin jami’ar kan zargin cin hanci da rashin adalci.

Halin da Dr. Ebong ya shiga bayan korarsa aiki

Duk da nasarorin da ya samu a kotu, har da hukuncin Kotun Daukaka Kara a watan Disamba 2024, jami’ar ba ta dawo da shi bakin aiki ko biyansa hakkokinsa ba.

Saboda kwashe tsawon lokaci ba aiki, Dr. Ebong ya fuskanci talauci, har ta kai ga ba ya iya sayen magani domin kula da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Atiku: Gwamna ya fadi dalilin Gwamnonin PDP na watsi da kawancen jam'iyyu

An gano cewa yana fama da matsananciyar cutar zuciya a 2020. Fitaccen attajiri, Femi Otedola, ya shiga cikin lamarin domin taimaka masa bayan rahoton Premium Times.

Rahoto ya nuna cewa ya yi jinya a asibiti mai zaman kansa a Uyo, inda ya fara murmurewa, sai dai ciwon ya sake tasowa a wstan Fabrairu.

An tattaro cewa bayanin da likitansa ya yi ne ya sa aka kai shi Asibitin Koyarwa na UniUyo a watan Maris.

UniUyo.
Ana zargin jami'ar UniUyo da yi wa marigayin rashin adalci Hoto: UniUyo
Asali: Facebook

An zargi jami'ar Uni Uyo da zaluntar marigayin

A ranar Lahadi, 13 ga Afrilu, Dr. Ebong ya kira wani dan jarida yana cewa: “Na zauna a nan tsawon lokaci. Kamar ina gidan yari. Ina so in koma gida.”

Lauyan kare hakkin dan Adam, Inibehe Effiong, ya taba ce wa a 2020 cewa:

"Idan Dr. Inih Ebong ya mutu ba tare da an yi masa adalci ba, haƙƙinsa zai koma kan hukumar gudanarwa da Majalisar Jami’ar Uyo.”

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon ɗan wasa kuma Kocin Super Eagles ya rasu a shekara 74

Marigayi Dr. Ebong dan asalin karamar hukumar Ibiono Ibom ne, ya yi karatunsa na sakandare a Etinan Institute, sannan ya samu digiri a Jami’ar Najeriya da kuma Jami’ar Birmingham a Ingila.

Farfesa a OAU ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, kun ji cewa Farfesa Jimoh Olanipekun, ɗaya daga cikin manyan malaman jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife ya mutu.

Rahotanni sun nuna cewa Farfesan ya kamu da rashin lafiya ne farat daya a yayin taron sashe-sashe na jami'ar OAU da aka gudanar.

Mai magana da yawun OAU ya ce ana tsakiyar taron, aka ga numfashin Farfesan ya fara canzawa daga bisani kuma ya yanke jiki ya faɗi, Allah ya masa rasuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng