An Taso Malamin Addini a Gaba kan Hudubar Cewa Annabi Isa na Ƙyamar Talakawa
- Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna Fasto Ibiyeomie yana cewa Yesu bai taba ziyartar talaka ba, yana kin talauci
- Fasto Abel Damina ya caccaki kalaman Ibiyeomie, yana cewa ya karkatar da sakon Yesu don son dukiya da tunanin arziki
- Rabaran Adegbite na CAN ya bayyana wa’azin a matsayin raina littafi mai tsarki, yana gargadin Kiristoci su guji “fastoci na bogi”.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jihar Lagos - Kungiyar Kiristocin Najeriya da shahararren Fasto Abel Damina sun soki Fasto David Ibiyeomie na Salvation Ministries kan wa’azinsa da ya soki talauci.
Damina da kungiyar CAN sun soki Faston ne bayan cewa Annabi Isa (AS) yana kyamar talakawa da talauci.

Asali: Getty Images
Fasto ya jawo hayaniya a huɗubarsa
A wani bidiyo da Ossai Ovie Success ya wallafa a shafin Facebook da ya karade intanet, Ibiyeomie ya ce Yesu bai taba ziyartar gidan talaka ba, alamar Allah ba ya son talauci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin addinin ya kara da cewa mutuwa da tashin Yesu ba don ceto ba kawai ba, har da ‘yantar da masu bi daga talauci da rashin fahimta.
Ya ce:
“Ya ziyarci Lazarus, ba talakawa ba ne, suna bashi abinci, ya shiga gidan Zakiyu mai arziki. Yesu na kin talauci, hakan ke nan.”
“Ya mutu don kada ku kasance talakawa, ba laifi ne mutum ya shigo coci a matsayin talaka ba, amma bai kamata ya ci gaba da haka ba.”
An yi wa Fasto raddi kan kalamansa
Fasto Damina na 'Power City' ya mayar da martani cikin bidiyo, yana cewa Ibiyeomie ya karkatar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da son arziki.
Damina ya bayyana Ibiyeomie a matsayin mai kokarin cin moriyar wa’azi don samun kudi, yana kiran kalamansa da cin mutuncin Littafi.
Ya kuma zargi Ibiyeomie da karkatar da sakon Yesu domin burin duniya da kudi, yana cewa wannan ba shi ne addinin gaskiya ba.
A cewarsa:
“Yaya Yesu zai ki talaka? Ya kasance mai arziki, amma saboda mu ya zama matalauci. Arzikinsa rahama da adalci ne, ba kudi ba.
“Tun daga haihuwarsa, Yesu ya kasance tare da talakawa, da yana kin talakawa, da ba zai zo haka ba.”

Asali: Facebook
Kungiyar CAN ta caccaki Fasto kan hudubarsa
Shugaban CAN a jihar Lagos, Rabaran Stephen Adegbite, ya ce kalaman Ibiyeomie sun raina gaskiya, kuma suna karkatar da manzancin Kristi.
Ya bayyana wa’azin a matsayin barazana ga koyarwar Kiristanci, yana cewa hakan magana ce mara tushe kuma ya kamata Kiristoci su kula.
Adegbite ya ja kunnen Kiristoci da ka da su yarda da wa’azin “fastoci na bogi” da ke fifita dukiya fiye da gaskiya da ceton rai.
Ya ce:
“Ya kamata ya gaya wa mutane gaskiya kawai. Yesu masoyin talakawa ne, hakan yana daga cikin dalilin zuwansa duniya.
Tsofaffin Fastoci sun bar addinin Kiristanci
Kun ji cewa bayan daukar shekaru da dama suna ibada da imani mai karfi ga Ubangiji, wasu ‘yan Najeriya sun yanke shawarar barin addinin Kiristanci.
Tsofaffin Fastocin sun yi haka ne bayan bincike da tunani mai zurfi kamar yadda suka sanar a lokacin da suka rungumi Kiristanci.
Sun fito a kafafen sada zumunta suka sanar da ficewarsu daga addinin ba tare da damuwa da martanin mutane ba.
Asali: Legit.ng