Buba Galadima Ya Taso Buhari a Gaba, Ya Fadi Yaudarar da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

Buba Galadima Ya Taso Buhari a Gaba, Ya Fadi Yaudarar da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

  • Buba Galadima ya yi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo kan yadda ya tafiyar da mulkinsa
  • Tsohon makusancin na Buhari ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan ya ɓoye ainihin manufarsa ga ƴan Najeriya
  • Buba Galadima ya nuna cewa Buhari shi ne babbar yaudarar da ta taɓa faruwa ga Najeriya domin ya nuna yana tare da talakawa amma ashe ba haka ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon makusancin Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya yi kalamai masu kaushi kan tsohon shugaban ƙasan.

Buba Galadima ya bayyana cewa Buhari shi ne babbar yaudarar da ta ɓa faruwa ga Najeriya.

Buba Galadima ya caccaki Buhari
Buba Galadima ya soki Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari, Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba Galadima ya ce Buhari ya yaudari ƴan Najeriya

Jigon na jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa Buhari ya ɓoyewa ƴan Najeriya ainihin abin da ke zuciyarsa, sai da ya hau mulki sannan ya fara gana musu azaba.

Ya bayyana cewa a halin yanzu, tsohon shugaban ƙasan bai da wani tasiri a siyasar Najeriya.

Buba Galadima ya nuna mamakinsa kan yadda wasu ƴan siyasa suke tururuwar zuwa wajen tsohon shugaban ƙasan.

"Buhari bai da wani tasiri a siyasar Najeriya yanzu. Atiku ya doke shi a zaɓen 2019. Saboda kawai ba su ayyana Atiku a matsayin wanda ya yi nasara ba, ba yana nufin bai ci zaɓen ba."
"Idan na ga mutane suna kai ziyara wurin Buhari, sai na yi dariya kawai. Wane ne Buhari? Ya kamata ya je ya huta kawai ya jira ajalinsa, ya fara yawan yin Astaghfirullah (neman gafarar Allah) saboda ya ci amanar ƴan Najeriya."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya ce Buhari mutum ne na bogi

Jigon na jam'iyyar NNPP ya ƙara da cewa tun da farko ya gano cewa Buhari mutum ne na bogi, amma aka ba shi shawara kan ya ci gaba da tafiya tare da shi.

Buba Galadima
Buba Galadima ya caccaki Muhammadu Buhari Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook
"Ni ne mutum na huɗu a jerin mutanen da suka sa hannu a takardar kafa jam’iyyar APC. Amma daga baya na gano cewa Buhari shi ne mafi girman yaudarar da ta taɓa faruwa a Najeriya."
"Mutum ne na bogi. Na gane hakan tun da wuri, amma ubangidana kuma abokin shawarata, Sule Hamma, kullum yana bani shawara a matsayinsa na babba a gareni."
"Buhari ya zama mafi girman yaudara ne saboda ya ɓoye ainihin manufarsa tsawon shekaru 15. Babu wani ɗan Najeriya da ya san abin da zai yi da zarar ya hau mulki."
"Ba mu san gaskiyar halayensa ba. Tsawon shekaru, Buhari yana shelar cewa yana tare da talakawa, ba tare da mun san cewa shi mai kare masu kuɗi da manya ne ba. Wannan ba babbar yaudara ba ce?"

- Buba Galadima

Buba Galadima ya faɗi dalilin yin saɓani da Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa Buba Galadima ya bayyana dalilin da ya sanya suka samu saɓani da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Buba Galadima ya bayyana cewa sun samu saɓani da Buhari ne saboda yawan faɗa masa gaskiya da yake yi.

Jigon na jam'iyyar NNPP ya nuna cewa kafin ya fice daga APC, Buhari ya kafa wani kwamiti domin a kore shi daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng