Malamin Addini Ya Fadi Tsarin Tinubu Wanda Ya Kara Yawaita Cin Hanci a Najeriya
- Primate Elijah Ayodele ya gargaɗi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan
- Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya nuna cewa rabon tallafin shinkafa da Tinubu yake yi, ƙara yawaita cin hanci kawai yake yi
- Ya gargaɗi shugaban ƙasan kan cewa ƴan Najeriya za su iya yin bore idan ba a ɗauki matakan da suka dace na rage wahala ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi gargaɗi ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Primate Ayodele ya yi kira ga shugaba Tinubu da ya ɗauki matakan magance matsalar tattalin arziƙin da ke fuskantar Najeriya.

Asali: Facebook
Jaridar Tribune ta ce malamin addinin ya bayyana hakan ne yayin da yake fitar da hasashensa kan shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayodele ya gargaɗi Bola Tinubu
Primate Ayodele ya yi hasashen cewa ƙasar nan za ta fuskanci mawuyacin hali na tattalin arziƙi a wannan shekara idan gwamnati ta gaza wajen ɗaukar matakan da suka dace.
Malamin addinin ya yi hasashen matsin tattalin arziƙi, inda farashin kayan masarufi za su yi tashin gwauron zabi.
Ya soki shirin rabon tallafin shinkafa na shugaba Tinubu, inda ya ce hakan yana ƙara yawaita cin hanci ne, kuma bai maganin talauci ko wahalar rayuwa.
Ya yi kira ga gwamnati da ta buɗe iyakokin ƙasar nan da kuma bunƙasa aikin gona domin rage matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi.
Me malamin ya ce kan cin hanci a mulkin Tinubu?
Malamin addinin ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin tattalin arziki, ƴan Najeriya na iya bijirewa su yi zanga-zanga mai muni.
"Ƴan Najeriya ka da su bari a yaudare su, za mu fuskanci matsanancin matsin tattalin arziƙi a wannan shekara saboda gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba."

Kara karanta wannan
Malami ya faɗi jihohi 8 da ƴan bindiga ke shirin kai hari, ya ce rayuwar sarki na cikin haɗari
"Misali, ba a buɗe iyakokinmu ba a hukumance, kuma saboda haka abubuwa suna ƙara wahala. Ka da mu yaudari kanmu."
“Farashin mai zai sauka, amma ba yanzu ba, mu shirya sayen mai kan N1,200. Shinkafar gida za ta kai N100,000, yayin da shinkafar waje za ta kai N140,000. Sauran kayan abinci kamar doya, wake, da man gyada za su ci gaba da tsada."
“Shirin rabon tallafin shinkafa kawai yana kara yawaitar cin hanci ne, ba ya rage wahala ko kaɗan sai dai ma ya ƙara ta."
"Wannan wahalar ba daga sama take ba, aiki ne na mutanen da ke kan madafun iko. Ba na ganin wannan yunwar za ta ƙare nan ba da daɗewa ba, domin wahala za ta mamaye kowane fanni."
“Kamar yadda na faɗa a baya, idan gwamnati ba ta yi taka-tsan-tsan ba, mutane za su fara jifar su. Ya kamata su kafa kwamitoci da za su tunkari waɗannan matsaloli daga kowane ɓangarori kafin abin ya zama wani abu daban."
- Primate Ayodele
Ayodele ya faɗi hanyar kifar da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Primate Elijah Ayodele ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su bi domin kayar da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Shugaban na cocin INRI Evangelical Spiritual ya bayyana cewa dole ƴan adawa su yi haɗaka idan suna son ƙwace mulki a hannun Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng