Dokar Ɓatanci: Shehi Ya Yi Zazzaga ga ECOWAS, Ya Kira Abba Kabir a Addu'o'insa

Dokar Ɓatanci: Shehi Ya Yi Zazzaga ga ECOWAS, Ya Kira Abba Kabir a Addu'o'insa

  • Fitaccen malamin Musulunci, Adam Abdallah Kano, ya soki ECOWAS kan dokar hana daukar mataki idan aka ɓata sunan Annabi Muhammad (SAW)
  • A cikin wani bidiyo da aka wallafa a Facebook, malamin ya yi ruwan addu'o'i da tsinuwa ga shugabannin kungiyar ECOWAS saboda hukuncin kotunsu
  • Ya ce kungiyar ta fitar da doka cewa kada a dauki mataki, ko daga kotu ko daga mutane, idan an yi batanci ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (SAW)
  • Malamin addinin ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kin amincewa da dokar, inda ya masa addu'a da fatan samun nasara a mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Fitaccen malamin Musulunci a Kano ya yi zazzaga ga Kungiyar ECOWAS kan hukuncin da kotunta ta yanke a yan kwanakin nan.

Sheikh Adam Abdallah Kano ya yi ruwan addu'o'i ga kungiyar da masu goyon bayanta kan dokar batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Sheikh ya yi Allah wadai da hukuncin kotun ECOWAS kan dokar ɓatanci
Sheikh Adam Abdallah Kano ya caccaki matakin kotun ECOWAS kan dokar ɓatanci. Hoto: Karatuttukan Malaman Musulunci, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Dokar ɓatanci: Sheikh Adam ya soki kotun ECOWAS

Hakan na kunshe a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a manhajar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, malamin ya yi Allah wadai da matakin kungiyar game da dokar ɓatanci ga Ma'aiki (SAW).

Malamin ya tsinewa shugabannin kungiyar tun daga kasa har zuwa matakin kololuwa saboda neman rage darajar Manzon Allah (SAW).

A cewarsa:

"Wata kungiya wai ECOWAS ta fitar da sanarwa cewa idan aka ɓaci Annabi SAW to ka da a sake daukar wani mataki.
"Mataki ko na kotu ko kuma wanda mutane za su dauka a hannunsu, sun kafa wata doka kan haka, kawai idan an ɓaci Annabi daidai yake da kowa haka maganar za ta tafi a banza.
"Daga darektan kungiyar har zuwa dan autanta, Allah ya kwashe musu albarka gaba daya, ya wargaza aniyasu da duk wani shirinsu."

Shehi ya yabawa Abba Kabir kan dokar ɓatanci a Kano
Sheikh Adam Abdallah Kano ya jinjinawa Abba Kabir kan matsayarsa game da dokar ɓatanci. Hoto: @ecowas_cedeao, @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Sheikh Adam ya yabawa Abba Kabir Yusuf

Malamin ya yi jinjina ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano kan matsayarsa game da hukuncin kotun ECOWAS.

Shehin ya yi masa ruwan addu'o'i na musamman domin samun farin ciki da kuma albarka a mulkinsa saboda matsayarsa.

"A lokacin ne kuma muke jinjina ta gaske ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, Allah ya saka masa da alheri ya faranta masa rai.
"Ya ce wannan doka mun yi watsi da ita, babu ruwanmu da ita, shi ne gwamna na farko da ya fito ya yi watsi da wannan doka kuma ya ce ba za ta yi aiki a Kano ba."

Abba Kabir ya soki ECOWAS kan dokar ɓatanci

Kun ji cewa gwamnatin Kano ta bayyana cewa ba za ta janye dokokin batanci ba, duk da hukuncin kotun ECOWAS da ke adawa da hakan.

Kotun ECOWAS ta bayyana cewa wasu sashe na dokokin Kano sun sabawa ka’idar kare hakkin bil’adama, lamarin da ya tayar da ƙura.

Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Ibrahim Waiya, ya ce dokokin na kare addini ne kuma suna wakiltar muradin al’ummar Musulmi na jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.