"An Samu Nasara": Abin da Ya Faru da Tawagar Gwamnatin Najeriya Ta Je Jamhuriyar Nijar
- Tawagar Najeriya karkashin ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ta gana da tawagar gwamnatin Jamhuriyar Nijar a birnin Niamey
- Taron ya maida hankali kan yadda ƙasashen biyu masu maƙwaftaka da juna za su fargaɗo da hulɗar diflomasiyya da ta taɓarɓarewa bayan juyin mulki
- A wata sanarwar haɗin guiwa da ɓangarorin biyu suka fitar, sun bayyana abubuwan da aka cimma wa a taron da aka yi ranar Laraba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niamey, Niger - Tawaga daga Najeriya tare da ta wakilan Jamhuriyar Nijar sun gana a Niamey ranar Laraba a wani yunƙuri na farfado da huldar diflomasiyya.
Gwamnatin Najeriya ta aika tawaga ta musamnan da nufin farfaɗo da dangantakar da ta tabarbare sakamakon juyin mulkin da ya faru a Nijar a watan Yulin 2023.

Asali: Twitter
Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Yusuf Tuggar, ne ya jagoranci tawagar da ta isa Niamey tun ranar Talata, kamar yadda hadiminsa Alkasim Abdulƙadir ya tabbatar a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta tura tawaga kasar Nijar
Ambasara Yusuf Tuuggar ya isar da saƙo na musamman daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa Shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani.
Tawagar ta kunshi manyan jami’an diflomasiyya, masu ba da shawara, da jami’an haɗin gwiwar tsaro.
Ministan Harkokin Waje na Nijar, Bakary Yaou Sangaré shi ne ya jagoranci tawagar gwamnatin sojin ƙasar a wannan zama da aka yi a birnin Niamey.
Najeriya da Nijar sun dawo da dangantakarsu
A cikin ganawar, an tattauna muhimman batutuwa kamar haɗin kan tsaro, cinikayya tsakanin iyakoki, ci gaban tattalin arziki, da inganta huldar diflomasiyya.
A cewar wata sanarwa da bangarorin biyu suka fitar, ganawar ta gudana cikin yanayi na fahimta da girmamawa, inda aka maida hankali kan matsalolin da kasashen ke fuskanta a matakan ƙasa da ƙasa.
Bangarorin biyu sun bayyana ƙudurin su na farfado da kwamitin haɗin gwiwa na Najeriya da Nijar (NNJC), domin dorewar dangantaka da ciyar da huldar kasashen gaba.
Abin da ya faru a taron Najeriya da Nijar
Sanarwar ta ce:
“Ƙasashen biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa na bai ɗaya da za su ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnatocin Najeriya da Nijar.
"Daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna akwai farfado da Kwamitin Haɗin Gwiwa na Najeriya da Nijar (NNJC), wanda zai ƙarfafa abubuwan da aka cimma zuwa yanzu.
An jaddada bukatar haɓaka haɗin gwiwar tattalin arziki a fannin kasuwanni, hanyoyin sadarwa, sufurin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maradi, bututun iskar gas, da sauran ayyuka da suka haɗa da noma, kiwo, ilimi da fasahar zamani.

Asali: Twitter
An tattauna batun tsaro a Najeriya da Nijar?
A ɓangaren tsaro, Ministocin biyu sun nuna damuwa kan barazanar ta’addanci da ke addabar iyakokin kasashen biyu, wanda ke zama cikas ga aiwatar da shirye-shiryen raya ƙasa.
Daga nan ne suka buƙaci ma’aikatun tsarona ƙassshen biyu su ci gaba da aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya.
Ministocin sun kuma cimma matsaya kan kafa Kwamitin Tattaunawa na Hadin Gwiwa domin magance ƙalubale da habaka damammaki don amfanin jama'ar kasashen biyu.
Najeriya na shirin tura jadaku ƙasashen waje
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta kammata tantance jakadu 109 da za ta tura zuwa kasashe daban-daban.
An ruwaito cewa sun tabbatar mata da cewa an kammala binciken tsaro da tarihin kowanne daga cikin wadanda aka mika sunayensu.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai mika sunayen ga Majalisar Tarayya domin tantance su da tabbatar da naɗinsu a hukumance.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng