Gwamnatin Benue Za Ta Kori Fulani Makiyaya Daga Jihar Ta Kan Wani Dalili 1 Tak

Gwamnatin Benue Za Ta Kori Fulani Makiyaya Daga Jihar Ta Kan Wani Dalili 1 Tak

  • Gwamnatin jihar Benue ta ba wa makiyaya wa'adi kwanaki 14 da su dina yin kiwon dabbobi a fili ko kuma su fuskanci hukunci
  • MajaliMajalisar tsaro ta jihar ce ta yanke wannan hukuncin a ranar Talata inda ta ce za ta hukunta masu ba makiyayan mafaka
  • Akwai wata doka da ta hana kiwo a fili a jihar da aka yi a 2017 wadda yanzu Gwamna Hyacinth Alia zai yi amfani da ita

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Benue - Majalisar tsaro ta jihar Benuwe ta baiwa makiyaya wa'adin kwanaki 14 da su daina kiwon dabbobi a fili ko kuma su fuskanci hukunci.

Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, Gwamna Hyacinth Alia ne ya jagoranci taron majalisar tsaron jihar.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Gwamnatin Benue ta ba wa makiyaya wa’adin kwana 14 su dena kiwo a fili
Gwamnatin Benue ta ba wa makiyaya wa’adin kwana 14 su dena kiwo a fili. Hoto: @benuestategovt
Asali: Twitter

Dokar jihar Benue da ta haramta kiwo a fili

Majalisar ta yanke shawarar cewa dole ne makiyaya su bi dokar hana kiwo a fili ta jihar da aka yi a 2017, tana mai jaddada cewa har yanzu dokar tana aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta kuma kafa wani kwamiti mai mutum bakwai da zai tabbatar makiyayan ba su tsallake wa'adin da aka ba su ba tare da kama wadanda suka sabawa dokar.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sir Tersoo Kula ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati da ke Makurdi a daren ranar Talata.

Gwamnati ta nemi taimakon al'ummar jihar

Majalisar ta kuma yi kira ga makiyayan da suka shiga jihar a 'yan kwanakin nan tare da shanunsu suna kiwo a fili da su gaggauta ficewa daga jihar su koma inda suka fito.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa aka fitar da Murja Kunya daga gidan gyaran hali, gwamnatin Kano ta magantu

A hannu daya, majalisar ta bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu domin gwamnatin jihar na kokarin tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar baki daya.

Don haka majalisar ta nemi jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran jama’a da su kai rahoton duk ke da dabi’ar hada kai da kuma gayyatar makiyaya zuwa cikin jihar.

Gwamnati za ta kawo karshen fadan makiyaya da manoma

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bullo da wani shiri da ta yi wa take da 'Pulaku' da nufin kawo karshen manoma da makiyaya a fadin Najeriya.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya kaddamar da shirin a Abuja ya ce ba iya fadan makiyayi da manoma ba, shirin zai inganta tsaro da hadin kan 'yan kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel