Lailatul Kadri: Sheikh Daurawa Ya Jero Falalar Goman Karshe na Azumin Ramadan
- Yayin da ake kokarin kammala azumi, Sheikh Daurawa ya ce goman ƙarshe na Ramadan sun fi falala fiye da sauran kwanaki a cikin watan
- Malam Daurawa ya jaddada darajar daren Lailatul Kadri wanda yayi daidai da watanni 1,000 na bauta kamar yadda malamai suka tabbatar
- Malamin ya bayyana muhimmancin shiga Itikafi don gyara dangantaka da Allah da kuma neman yafiya daga Ubangiji kan kura-kurai da mutum ya aikata
- Ya ce Annabi Muhammad (SAW) yana ƙara dagewa da raya dare da tashin iyalansa a goman ƙarshe domin kara kusanci da Ubangiji SWT
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Babban malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayani mai zurfi kan daren goman karshe a Ramadan.
Sheikh Daurawa ya jero falalar goman karshe da aka shiga yanzu a watan Ramadan saboda muhimmancinsu ga dukan Musulmi mai azumi.

Asali: Facebook
Goman karshen Ramadan: Daurawa ya shawarci Musulmi
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da BBC Hausa ta wallafa a shafin X a yau Laraba 19 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon mai tsawon mintuna uku, Daurawa ya fadi falalar daren goman karshe da muhimmancinsa kamar yadda Musulunci ya tabbatar.
Legit Hausa ta bibiyi faifan bidiyon inda ta samu muku wasu muhimman abubuwa da ke tattare da goman karshe na Ramadan da muke ciki.
1. Fifiko da aka ba goman karshe a Ramadan
Malam Daurawa ya ce daren goman karshe na da abubuwa masu muhimmanci a cikinsa wanda ya sa ake fifita su fiye da goman farko da na tsakiya.
Ya ce farko dai Allah ya yi rantsuwa daren a cikin Kur'ani kamar yadda wasu malamai suka fassara ayar cewa sune goman karshe na watan Ramadan.
Har ila yau, ya bayyana alfanun da daren ke da shi idan aka kwatanta da sauran dararan Musulunci saboda muhimmancin da daren ya kunsa da albarka.
2. Daren Lailatul kadri na Ramadan
Malamin ya yi bayani kan daren mai daraja inda ya ce idan mutum ya dace da ita kamar ya shafe watanni 1,000 yana bautar ubangiji.
Daga cikin dararan idan mutum ya dace a daren 21 ko 23 ko 25 ko 27 ko kuma daren 29 kamar ya yi shekara 84 da watanni yana bauta kenan.
Shehin malamin ya shawarci Musulmai ka da su yi wasa da wannan daren saboda yadda aka dunkukle ibadar wata dubu a dare daya.

Asali: Facebook
3. Shiga Itikafi a masallaci yayin Ramadan
Sheikh Daurawa ya bayyana yadda Itikafi yake inda ya ce mutum ne zai tashi ya koma kaco-kan a masallaci musamman saboda bauta.
Ya ce ana shiga Itikafi saboda mutum ya yi tuntuntuni kan farkonsa da karshensa wurin yin ibada da karatun Kur'ani.
Malamin ya ce akalla ana son mutum ya yi na kwana daya ko biyu ko uku ko kuma na kwanaki 10 domin gyara alaka da Ubangiji da neman gafarar ubangiji.
Yadda Annabi (SAW) ke ibada a goman karshe
Sheikh Aminu Daurawa ya ce Annabi Muhammad (SAW) idan goman karshe ya zo ya kan yi abubuwa kamar guda uku wadanda ke nuna darajar da daren ke da shi ga al'ummar Musulunci.
Na farko, ya kan zage dantse duk da kullum a cikin ibadah yake amma ya kan dage a kan dagewar da yake yi domin amfanin da ke tattare da daren.
Na biyu, Annabi (SAW) ya kan yi sallah, ya yi barci amma a karshen Ramadan ya na raya daren ne gaba daya saboda nuna muhimmancinsu ga al'ummarsa.
Na uku, fiyayyen halitta ya kan tashi iyalansa domin su yi ibadah domin dacewa da wannan dare mai albarka.
Sheikh Daurawa ya jero alamomin lalacewar matashi
Kun ji cewa Malamin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa ya jero hanyoyin da ake gane matashi ya fara lalacewa wanda sai an dage kafin a taro shi daga hanyar da ya fara bi.
Malamin ya ce duk matashin da ba ya Sallah yana da babbar alamar lalacewa, musamman idan yana gudunta a kowane lokaci.
Sheikh Daurawa ya kuma lissafo rashin zuwa makaranta, ko dai ta boko ko ta addini, ya na daga cikin manyan alamomin matashin da ke shirin lalacewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng