Lailatul Qadr: Yadda Musulmi zai Ribaci Kwanaki 10 na Karshen Ramadan

Lailatul Qadr: Yadda Musulmi zai Ribaci Kwanaki 10 na Karshen Ramadan

Ana bukatar kowane Musulmi ya dage da ibada a kwanaki 10 na karshen watan Ramadan domin tara lada mai yawa da neman yardar Allah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadan suna da matuƙar daraja a cikin addinin Musulunci.

Sheikh Usman Muhammad Al-Juzri ya bayyana cewa waɗannan kwanaki suna da falala domin su ne mafi daraja a cikin watan Ramadan.

Al-Juzuri
Muhimman abubuwa kan kwanki 10 na karshen Ramadan. Hoto: Hoto: Muhammad Babayo Aliyu
Asali: Facebook

A hira da ya yi da Legit Hausa, Malamin ya ce kowanne Musulmi da ya samu damar ibada a kwanakin, ya samu wata dama da zai samu riba mai yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A karkashin haka, Sheikh Al-Juzuri ya ce bai kamata wani Musulmi ya yi kasa a gwiwa ba matukar yana da lafiya da damar yin ibada a kwanakin.

Kara karanta wannan

'Za a iya samun karamin yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta sun gargadi Tinubu

Falalar daren Lailatul Qadri

Sheikh Al-Juzri ya bayyana cewa Allah ya fifita daren Lailatul Qadri a cikin kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadan.

A cewarsa, wannan dare yana da matuƙar albarka kuma yana da falaloli da suka haɗa da:

  1. Saukar da Al-Kur'ani: Malamin ya ce a cikin daren aka saukar da Al-Kur'ani mai girma, saboda haka ya kamata a rika karanta shi sosai.
  2. Daren ya fi wata 1,000: A cewar Al-Kur'ani, yin ibada a daren Lailatul Qadri ya fi wata 1,000 daraja.
  3. Albarka ta musamman: Allah ya bayyana cewa wannan dare yana da albarka ta musamman ga masu ibada.
  4. Mala'iku na saukowa: Mala’iku suna saukowa a cikin daren da albarka da rahamar Allah.
  5. Aminci a cikinsa: Allah ya tabbatar da cewa wannan dare cike yake da aminci har zuwa wayewar gari.
  6. Tsara al’amuran shekara: A cikin daren ne Allah ke tsara dukkan al’amuran da za su faru a shekara.
  7. Gafarar zunubai: Duk wanda ya tsayu da ibada a daren da ikhlasi, Allah yana gafarta masa zunubansa.

Kara karanta wannan

El Rufai ya tuno shekaru 8 na mulkinsa, ya fadi abubuwa 4 da ya fi jin dadinsu

Al-Juzuri
Sheikh Al-Juzuri yana tafsiri. Hoto: Muhammad Babayo Aliyu
Asali: Facebook

Yadda za a ribaci kwanakin 10 na karshen Ramadan

Sheikh Al-Juzri ya ce Annabi (SAW) ya na ƙoƙarin yin ibada a cikin waɗannan kwanaki fiye da yadda yake yi a sauran kwanakin Ramadan.

Ya bayyana cewa wasu magabata na ganin cewa yawaita addu’a shi ne mafi falala a daren Lailatul Qadri.

A cewarsa, maimakon mutum ya zaɓi wasu kwanaki daga cikin 10 na ƙarshe, yana da kyau ya yi ƙoƙarin raya su gaba ɗaya.

"Idan an ce a raya dararen ba ana nufin mutum ya kwana yana ibada ba ne, abin da ake nufi shi ne mutum ya zabi wasu lokuta yana ibada a cikinsu"

- Sheikh Al-Juzuri

Malamin ya kuma bukaci Musulmai su guji sakaci wajen yin ibada a waɗannan kwanaki domin samun rahama da gafarar Allah.

Makka
Musulmai na ibada a masallacin Ka'aba. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Bukatar wayar da kan jama’a

A ƙarshe, Sheikh Al-Juzuri ya bukaci musulmai su riƙa sanar da juna falalar kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Albarkacin azumi: Yadda almajirai suka yi cudanya da gwamnan Nasarawa

Ya ce yana da kyau a yada ilimi da alheri a tsakanin mutane domin su ribaci wannan dama ta musamman.

"Duk wanda ya san wani abu na ilimi a kan kwanaki 10 na karshen Ramadan, ya kamata ya sanar da wasu.
"Yana da kyau a ribaci kafafen sada zumunta wajen tunatar da al'umma falalar kwanakin."

- Sheikh Al-Juzuri

Malamin ya jaddada cewa duk wanda Allah ya ba damar samun kwanaki 10 na karshen Ramadan ya samu damar gyara ayyukansa, ,musamman idan ya yi sakaci a farkon watan.

Sallah
Musulmai na sallah a masallaci. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa Malamin Musulunci, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwani ya rasu bayan fama da ya yi da rashin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya rasu ne bayan ya cika shekaru 69 da haihuwa kuma an masa janaza a ranar Talata, 18 ga watan Ramadan, 1446.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng