Abin da Daurawa Ya Ce ga Yan Uwan Dan TikTok, Yahaya America, Ya Shawarci Al'umma
- Aminu Ibrahim Daurawa ya jinjinawa iyalan Yahaya America bisa matakin da suka dauka kan danuwansu, yana mai cewa sun taimaka wurin dakile badala
- Shehin malamin ya bukaci sauran iyalai su yi koyi da wannan mataki, yana mai bayyana cewa hakan ne mafita ga matsalar yada badala a kafofin sadarwa
- A madadin hukumar Hisbah, Sheikh Daurawa ya mika godiya tare da yi wa iyalan addu'a, yana rokon Allah ya kara dora su a kan hanya madaidaiciya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Shugaban hukumar Hisbah a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya magantu kan matakin da wasu iyalai suka dauka kan dansu.
Daurawa ya jinjina wa iyalan gidansu dan TikTok, Yahaya Yau Kura (America) wanda yake kalaman batsa a kafofin sadarwa.

Asali: Facebook
Aminu Daurawa ya jinjina wa iyalan Yahaya America

Kara karanta wannan
'Shi zai iya gyara Najeriya': Dan PDP ya roki Kwankwaso, Obi su hade da Atiku Abubakar
Shehin malamin ya bayyana haka ne a cikin wata murya da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin muryar, Daurawa ya bukaci sauran al'umma da su rike koyi da irin wannan mataki da iyalan gidanku dan America suka yi.
Sheikh Daurawa ya ce a madadin hukumar Hisbah a Najeriya suna matukar godiya saboda sun taimaka wurin dakile badala.
"Assalamu Alaikum, sunana Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, Kwamanda Janar na hukumar Hisbah ta Kano.
"Ina mika godiya a madadin yan Hisbah na kasa baki daya bisa matakin da wasu dangi duka ɗauka kan dansu da ke aikata badala a kafofin sadarwa.
"Wannan mataki da suka ɗauka shi ne ya kamata ko wace al'umma da unguwa da iyalai ya kamata su dauka domin dakile badala.
"Saboda haka muna jinjina da addu'ar fatan alheri ga wadannan iyalai da suka dauki wannan mataki na kawar da badala."
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Daurawa ya shawarci iyalai a Najeriya
Sheikh Daurawa ya yi musu fatan alheri tare da shawartar sauran iyalai da su yi koyi da wannan mataki da suka ɗauka.
Daga bisani, bayan godiya ya yi addu'ar Allah ya kara dora su a kan daidai ya kuma gafarta wa mahaifinsu da ya rasu.
Daurawa ya fadi alamomin lalacewar matashi
Kun ji cewa Sheikh Aminu Daurawa ya ce matashin da ba ya sallah yana da babbar alamar lalacewa, musamman idan yana gudunta.
Rashin zuwa makaranta, ko dai ta boko ko ta addini, yana daga cikin manyan alamomin matashin da ke shirin lalacewa.
A cikin wani bidiyo Sheikh Daurawa ya lissafa alamomi biyar na lalacewar matashi ciki har da rashin sana'a da shaye-shaye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng