Kano: Duk da Umarnin Kotu, Gwamna Abba Ya Umarci Masarautu Su Shirya Hawan Sallah
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin cewa masarautun jihar guda hudu su shirya gudanar da hawan Sallah karama
- Wannan umarni ya zo ne a lokacin taron buda baki na Ramadan da aka gudanar tare da Sarakuna a Fadar Gwamnatin Kano a yammacin Talata
- Gwamnan ya bayyana cewa hawan Sallah na da matukar muhimmanci wajen nishadantar da al’umma da kuma inganta al’adun gargajiya
- Ya ce dukkan hukumomin tsaro na jihar za su kasance cikin shiri don samar da cikakken tsaro ga al’umma yayin gudanar da bukukuwan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya umarci masarautun jihar guda hudu da su shirya gudanar da hawan Sallah karama a bana.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a lokacin taron buda baki na Ramadan da aka yi tare da Sarakuna a Ante Chamber, Fadar Gwamnatin Kano, a ranar Talata.

Asali: Facebook
A sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya bayyana cewa hawan sallar na da muhimmanci, musamman wajen nishadantar da jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya fadi muhimmancin hawan sallah
Gwamna Abba ya ce jama’ar jihar na matukar sa ran ganin bikin Sallah, inda suke sanya sababbin kaya, suna cika tituna domin kallon Sarakunansu a kan doki, tare da sada zumunci.
Saboda haka, Gwamnan ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa ba za a hana jama’a wannan hakki nasu ba.
Ya tabbatar da cewa dukkan hukumomin tsaro na jihar za su kasance cikin shiri domin samar da cikakken tsaro ga jama’a yayin hawan bukukuwan sallah.

Kara karanta wannan
Abin da Abba Kabir ya fadawa malamai da ya faranta musu rai yayin buda baki a Kano
Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a kaddamar da majalisar masarautar Kano a watan Afrilu na wannan shekara domin ta fara aiki yadda ya kamata.
Har ila yau, ya ce za a bayyana ka’idoji, dokoki da sauran muhimman abubuwa da suka shafi majalisar a ranar da za a kaddamar da ita.
Gwamna Abba ya jinjinawa sarakunan Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa sarakunan Kano bisa kwarewa da dangantaka mai kyau da suka nuna tun bayan nadinsu.
Ya na ganin wannan ne karon farko a tarihin jihar da aka samu irin wannan girmamawa tsakanin sarakunan, musamman dangane da tsarin matsayi da daraja a masarautun.

Asali: Facebook
A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Masarautar Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da sauran sarakunan masarautun masu daraja ta biyu.
Ya kuma roki Gwamnan Kano da ya yi amfani da cibiyoyin gargajiya domin yada manufofi da shirye-shiryen gwamnati zuwa ga jama’a, domin tabbatar da aiwatar da su cikin sauki da inganci.

Kara karanta wannan
Albashi N500,000: 'Yan kasar Sin suka shigo Najeriya, sun kafa kamfanin sarrafa lithium a Nasarawa
Kotu ta yi hukunci kan masarautun Kano
A baya, kun samu labarin cewa kotun daukaka Kara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncinta na 10 ga Janairu, wanda ya amince da soke dokar kafa sababbin masarautu ta 2019.
Kotun ta bayar da wannan hukunci ne bayan sake duba shari’ar da aka yi, ta ce a jingine hukuncinta har sai kotun koli ta yanke hukunci a kan dambarwar masarautar jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng