Sanusi II Ya Yi Biris da Umarnin 'Yan Sanda, Ya Gudanar da Hawan Sallah

Sanusi II Ya Yi Biris da Umarnin 'Yan Sanda, Ya Gudanar da Hawan Sallah

  • Alhaji Muhammadu Sanusi II ya gudanar da hawan Sallah a Kano a matsayinsa na Sarkin Kano na 16
  • Mai martaba Sarkin ya gudanar da hawan ne bayan ya ja sallar Idi a masallacin Kofar Mata da ke cikin birnin Kanon Dabo
  • Gudanar da hawan dai ya saɓa da umarnin da ƴan sanda suka bayar inda suka haramta yin hawa a jihar domin a samu zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya gudanar da hawan Sallah domin bukukuwan babbar Sallah.

Sarkin na Kano ya jagoranci sallar idi inda ya yi huɗuba a masallacin Juma’a na kofar Mata.

Sanusi II ya yi hawan Sallah
Sanusi II ya yi hawan Sallah a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sanusi II ya yi sallar Idi a Kofar Mata

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

An gudanar da Sallar Idi a masallacin Juma'a na Kofar Mata sakamakon ruwan sama da ya mamaye harabar filin Idi wanda hakan ya sanya ba za a iya amfani da shi ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran muƙarraban gwamnatinsa sun gudanar da sallar Idin tare da Sarkin.

Sojoji, ƴan sanda da sibil difens da dai sauran su sun ba da tsaro.

Sanusi II ya yi hawan Sallah a Kano

Sarki Sanusi II ya bi hanyar da ya saba komawa gida, inda ya riƙa tsaya yana karɓar gaishe-gaishe daga wajen ɗaiɗaikun mutane sa ƙungiyoyi yayin da yake tafiya a kan doki.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da hana gudanar da hawan Sallah bayan wani taron tsaro na haɗin gwiwa da aka gudanar a jihar.

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin daɗinsa da matakin, inda ya nuna rashin jin dadin yadda ƴan sanda suka ɗauki wannan matakin ba tare da tuntuɓarsa ba a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: An bayyana jihar da Shugaba Tinubu zai yanka ragon layyarsa

Dalilin Ganduje na tsige Sanusi II

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya magantu kan musabbabin da ya sanya aka tsige shi daga kan sarautar Kano.

Sanusi II ya zargi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tuɓe masa rawani kawai saboda dalili na siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng