Barau Ya Girgiza SDP bayan Komawar El Rufai, Ɗan Takarar Gwamnan Kano Ya Koma APC
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi manyan jiga-jigan jam’iyyar SDP da suka sauya sheka zuwa APC
- Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Injiniya Yusuf Buhari, da ɗan takarar gwamnan Kano, sun koma APC tare da shugabanni 38
- Sanata Barau ya ce wannan sauya shekar ya tabbatar da rugujewar shirin amfani da jam'iyyar SDP a wajen kalubalantar APC a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi manyan jiga-jigan jam’iyyar SDP da suka sauya sheka zuwa APC.
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a 2023, Injiniya Yusuf Buhari, da ɗan takarar gwamnan Kano, Bala Muhammad Gwagwarwa, sun koma APC tare da wasu fitattun mambobin jam’iyyar.

Asali: Twitter
Jiga-jigan jam'iyyar SDP sun koma APC
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Sanata Barau ya ce ya karbi jiga-jigan SDP ne a wani gagarumin taro da aka gudanar a Otal ɗin REIZ Continental da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau ya ce wadanda suka sauya sheka sun haɗa da kwamitin zartarwa na SDP a jihar Kano, shugabannin ƙananan hukumomi 38, sakatarori, da kuma tsofaffin ‘yan takarar majalisar dokoki.
Mataimakin shugaban majalisar ya ce wannan mataki na sauya sheka yana nuna cewa an ruguza shirin amfani da SDP don kalubalantar APC a 2027.
"Masu tunanin za su yi amfani da SDP don cimma muradunsu sun gamu da cikas. Manyan ‘yan jam’iyyar sun koma APC don mara wa Tinubu baya," in ji Barau.
'APC ta kawo ci gaba a Najeriya' - Barau
Ya tabbatar wa sabbin mambobin cewa za a ba su cikakken dama a APC, yana mai cewa, "A jam’iyyarmu, kowa na da daraja, kuma ana yi wa kowa adalci."
Sanata Barau ya bayyana cewa shigowar waɗannan jiga-jigan siyasar APC wata alama ce ta cigaban da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke samu.
Ya bayyana cewa:
"Ina jin daɗin yadda ku ka fahimci irin ci gaban da ake samu kuma kuka zaɓi jam’iyyar da ke samar da mulki na gari a Najeriya."
Ya yaba wa Injiniya Yusuf Buhari, Bala Muhammad Gwagwarwa, da sauran waɗanda suka sauya sheka bisa yanke wannan shawara ta mara wa APC baya.
Sanata Barau ya jaddada cewa APC za ta cigaba da aiki tukuru domin tabbatar da ci gaban Najeriya.
'Yan Najeriya sun yi martani ga Barau
Bayan sauya shekar manyan jiga-jigan SDP zuwa APC, wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ci gaba.
@EngrKibiya ya rubuta cewa:
"A bayyane yake cewa SDP ta dakatar da Gwagwarwa tun bara, ba shi da wata alaƙa da jam’iyyar. Waɗanda suka koma APC ba don kishin jam’iyya suka yi ba, sai don kuɗi. Za su ɓace idan sun sami abin da suke so. Kano ba za ta amince da ku ba."
@Jibril5797262 ya ce:
"APC ce jam’iyya mafi lalacewa da rashin amfani a tarihi."
@Rashmus01 ya yi korafi da cewa:
"Abin takaici ne yadda sauya sheka ya zama sabon abin da ke daukar hankalinku, maimakon fifita bukatun masu zabe. Yanzu haka kuna ta murnar wasu sun sauya sheka. Allah ya kyauta."
@Abubaka38398542 ya rubuta cewa:
"Ba mu buƙatar mulkin APC a Najeriya, la’akari da yadda suka jefa mu cikin yunwa da fatara. Muna kira ga shugabannin da ke kishin ƙasa da su haɗa kai domin yakar zalunci a 2027."
@paschaleke ya yi martani da cewa:
"Hah! Sun fara rushe SDP kenan."
@ABDULKA19711300 kuwa ya bayyana cewa:
"SDP na gina sabuwar ƙawance mai ƙarfi da za ta hana APC sakat a 2027."
Duba sanarwar Sanata Barau a nan kasa:
El-Rufai ya fice daga APC, ya koma SDP
Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, matakin da ya tayar da kura a siyasar Najeriya.
El-Rufai ya ce ya bar APC ne saboda rashin adalci, yana mai alkawarin inganta dimokuradiyya tare da SDP domin ceto Najeriya daga hannun Shugaba Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng