Shin Bola Tinubu Ke Daukar Nauyin Jam'iyyar SDP da El Rufai Ya Koma?
- Fadar shugaban kasa da jam'iyyar SDP sun karyata zargin cewa Bola Tinubu ne ke daukar nauyin jam’iyyar adawa ta SDP
- Joe Igbokwe ya yi ikirarin cewa Tinubu ne mamallakin SDP, bayan ficewar El-Rufai daga APC zuwa SDP da aka yada a kafofin sadarwa
- Jigon SDP, Prince Adewole Adebayo da Daniel Bwala sun ce Tinubu bai da alaka da SDP kuma ba a taba danganta shi da jam’iyyar ba
- Wannan na zuwa ne bayan Nasir El-Rufai ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa SDP mai adawa a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa da wasu ‘yan siyasa sun bayyana ra’ayoyi daban-daban kan zargin cewa Shugaba Bola Tinubu ne ke daukar nauyin SDP.
Shafukan intanet da kafafen sada zumunta sun cika da zargin Joe Igbokwe na APC cewa Tinubu ne mamallakin jam’iyyar SDP.

Asali: Twitter
Ana zargin Tinubu ke daukar nauyin SDP
Dan takarar shugaban kasa a karkashin SDP a 2023, Prince Adewole Adebayo, ya musanta ikirarin da Igbokwe ya yi, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Joy Igbokwe ya ce masu buri na 2027 karkashin SDP su sani jam’iyyar tana karkashin ikon Tinubu ne.
Ya ce:
“Ina cewa idan har SDP tana nan, ku sani cewa Tinubu ne mai ita, ku yi watsi da shi ne ya zama muku damuwa."
Bayan cece-kuce da suka biyo bayan wannan rubutu, Igbokwe ya sake rubutu yana cewa, “Tinubu Sanata ne a SDP a 1993.”, cewar Daily Post.
Jam'iyyar SDP ta fede gaskiya kan zargin
Sai dai dan takarar shugaban kasa a SDP, Prince Adewole Adebayo, ya musanta ikirarin da Igbokwe ya yi.
A cewarsa:
“Waye shi? Ban san shi ba, ban kuma taba ganinsa ba, watakila yana zuba da baki ne kawai."

Asali: Twitter
Martanin Tinubu kan zargin mallakar jam'iyyar SDP
Fadar shugaban kasa ta karyata wannan ikirari, tana cewa ba zai yiyu SDP ta kasance mallakin Tinubu ba.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya ce Tinubu na da cikakken biyayya ga jam’iyyar APC.
A cewar Bwala:
“Ina tabbatar da cewa Asiwaju dan APC ne, shugaba ne a cikinta, kuma ba a taba cewa yana da alaka da SDP ba."
Bwala ya kara da cewa daga lokacin AD, AC, ACN har zuwa APC, ba a ta ba danganta Tinubu da SDP ba ko kadan har zuwa wannan lokaci da ake ciki.
Lamido ya soki El-Rufai kan kiransu SDP
Kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce Nasir El-Rufai ba ya da darajar shugabanci, ba zai iya janyo ‘yan PDP su bi shi jam'iyyar SDP ba.
Sule Lamido ya ce El-Rufai bai cancanci gayyatar manyan ‘yan adawa zuwa sabuwar jam’iyyarsa ba domin ba shi da kishin kasa.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa PDP ce ta haifi El-Rufai, bai kamata ya koma baya ya soke jam’iyyar da ta dauke shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng