Yadda ‘Dan Takarar Gwamnan Kano Ya Cire Rai Tun Kafin a Gama Tattara Sakamako

Yadda ‘Dan Takarar Gwamnan Kano Ya Cire Rai Tun Kafin a Gama Tattara Sakamako

  • Kafin a sanar da wanda ya ci zaben Gwamnan jihar Kano, ‘Dan takaran Jam’iyyar PRP ya hakura
  • Salihu Tanko Yakasai ya yarda ba zai kai labari ba, ya yi fatan alheri ga duk wanda zai yi nasara
  • Jam’iyyar LP ta ci kuri’u fiye da 5000 duk da Bashir I. Bashir ya sauya-sheka zuwa APC mai mulki

Kano - Kafin ayi nisa wajen tattara kuri’un sabon Gwamnan jihar Kano, Alhaji Salihu Tanko Yakasai wanda ya yi takara a jam’iyyar SDP, ya sallama.

Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu, ya yi magana a shafinsa na Twitter a safiyar Lahadi, yana mai nuna tuni ya rungumi kaddara.

Tsohon Hadimin Gwamnan na Jihar Kano yake cewa sun yi bakin kokarinsu wajen ganin sun samu nasara, amma Ubangiji bai nufa zai yi mulki ba.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Yakasai yake cewa duk da bai zama Gwamnan jihar Kano, ya samu karin masoya a rayuwarsa.

Jawabin Salihu Tanko Yakasai

"Yin kamfe na tsawon shekara daya abu ne mai wahalar gaske, amma mu ka jajirce a kan hanyar. Za a iya auna gogewa da ilmin da muka samu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mun godewa Allah Madaukakin Sarki da falalarsa a tsawon lokacin yakin neman zaben nan.

- Salihu Tanko Yakasai

Kano.
Dawisu ana kamfe a Kano Hoto: @Dawisu
Asali: Twitter

A jawabin da ya yi a dandalin sada zumuntan, Salihu Yakasai ya godewa danginsa, abokai, shugabannin jam’iyya da daukacin magoya bayansa.

Nagode da addu’o’inku da gudumuwar kudi, nagode da kalamai masu bada kwarin gwiwa. Wadannan abubuwa suka taimaka mani na kawo nan.

A lokacin an ji ‘dan takaran na PRP yana yi wa wanda zai zama Gwamna fatan alheri, kuma zai kai masa takardar manufofinsa domin ya yi aiki da shi.

Kara karanta wannan

Abba Gida-gida: Sabon gwamnan Kano ya yi magana, ya fadi abin da ya shiryawa Kanawa

Burin shi a cewarsa shi ne Kano ta cigaba, a karshe ya kare da yi wa Kanawa godiya ta musamman.

PRP, LP, da SDP

Legit.ng Hausa ta fahimci Salihu Yakassai ya tashi da kuri’u 2183 ne a zaben sabon Gwamnan. Bala Gwagwarwa na SDP yana bayansa da kuri’u 759.

‘Dan takaran LP, Bashir I. Bashir wanda ya koma goyon bayan APC, ya samu kuri’u 5409, yayin da INEC ta ce Muhammad Abacha ne ‘dan takaran PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel