Sokoto: 'Dan Majalisa Ya Dauki Nauyin Karatun Dalibai a Jami'a da Alawus duk Wata
- 'Dan Majalisar Tarayya daga jihar Sokoto ya dauki nauyin karatun dalibai a jami’a domin tallafa musu wajen samun ilimi mai inganci
- Shirin ya kunshi biya musu kudin makaranta gaba daya da aka zaba daga mazabarsa da ke jihar Sokoto a Arewacin Najeriya
- Baya ga kudin makaranta, za a rika ba wa daliban alawus har N30,000 duk wata domin taimaka musu wajen rayuwa a makaranta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - 'Dan majalisar Tarayya a jihar Sokoto, Hon. Sani Yakubu ya yi abin a yaba wa 'yan mazabarsa.
'Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gudu/Tangaza ya dauki nauyin karatun dalibai 21 zuwa jami'ar Al-Istiqama.

Asali: Facebook
'Dan majalisar Sokoto ya raba azumin Ramadan
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin ɗan majalisar, Hon. Munzali Lukman ya wallafa a shafin Facebook a yau Talata 18 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne makwanni uku bayan dan majalisar ya gwangwaje yan mazabarsa da abin alheri saboda azumin watan Ramadan..
'Dan siyasar mai wakiltar mazabar Gudu/Tangaza ya ba da tallafin N40m da buhuna 1,000 na shinkafa ga al’umma.
Hon. Sani Yakubu ya yi wannan abin alheri ne don saukaka wa al'umma yayin azumin watan Ramadan ya gabato.
Har ila yau, ya tabbatar da karin raba kayan abinci da tufafi kafin Sallah, tare da alkawarin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a yankin.
Hon. Sani Yakubu ya ba dalibai tallafi
Hon. Sani Yakubu ya gabatar da takardar shaidar gurbin karatu a jami'ar Al-Istiqama da ke jihar Kano ga ɗalibai 21 daga mazabarsa.
Sanarwar ta ce dan majalisar ya yi alkawarin biyansu N30,000 duk wata a matsayin kudin abinci.

Asali: Facebook
Al'umma sun yabawa ɗan majalisa a Sokoto
An tabbatar da cewa wannan shi ne karon farko a tarihin siyasar yankin da dan majalisar ya dauki nauyin karatun dalibai zuwa jami'a domin su yi karatu

Kara karanta wannan
Abin da Abba Kabir ya fadawa malamai da ya faranta musu rai yayin buda baki a Kano
Al'ummah Gudu/Tangaza sun yaba da wannan kokari na dan majalisar domin inganta harkokin ilimi.
Har ila yau, al'ummar sun yi addu'a ta musamman ga dan majalisar tare da rokon Allah ya saka masa alheri kan wannan babban aiki.
Legit Hausa ta yi magana da makusancinsa
Wani na kusa da ɗan majalisar, Abubakar Balle ya tabbatar wa wakilin Legit Hausa cewa Hon. Sani Yakubu zai dauki nauyinsu har su kammala karatu.
Balle ya ce a yau Talata an ba su takardar samun gurbin karatu a jami'ar Al-Istiqama da ke jihar Kano.
Matashin ya tabbatar da cewa an biyan kudin rijistarsu gaba daya, kuma ana sa ran za su tafi bayan salla idan Allah ya yarda.
Bauchi: Gidauniya ta dauki nauyin karatun dalibai
Kun ji cewa Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta raba fom na JAMB guda 300 ga dalibai da aka zaba daga yankin Bauchi ta Kudu.
Daliban sun fito daga kananan hukumomi bakwai, kuma an bi ka’ida wurin tantance wadanda suka fi cancanta.
An tabbatar da wanda ya ci jarabawar JAMB, Gidauniya za ta dauki nauyin karatunsa har zuwa jami’a ko kwalejin ilimi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng