Almundahana: An Sanya Ranar Da Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje Zai Bayyana Gaban Kotu

Almundahana: An Sanya Ranar Da Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje Zai Bayyana Gaban Kotu

  • Gobe Alhamis ne babbar kotu dake zamanta a jihar Kano za ta zauna kan tuhumar da gwamnati ke yiwa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje
  • Ana sa ran Abdullahi Ganduje, wanda shi ne shugaban APC a yanzu zai gurfana a gaban kotun domin sauraren tuhumar da ake yi masa
  • Baya ga Ganduje, ana fatan mai dakinsa, Hafsat Abdullahi Ganduje za ta bayyana bisa zargin almundahanar kudin mutanen Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- A ranar Alhamis, 11 Yuni, 2024 ne Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat da wasu mutum shida za su bayyana a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Alakar Jinsi: Gamayyar matasa sun yi zanga zangar kin LGBTQ da matsin rayuwa a Kano

Ana sa ran za su bayyana a gaban kotun da ke zamanta a Kano a gobe Alhamis, inda ake zarginsu da cin hanci da almundahanar biliyoyin kudade.

Abdullahi Ganduje
Ana sa ran Abdullahi Ganduje da mai dakinsa za su bayyana gaban kotu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Channels Television ta wallafa cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shigar da kara gaban Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu kan zargin Ganduje da cin zarafin ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da safe za a saurari shari'ar Ganduje

A safiyar ranar Alhamis da misalin karfe 10.00a.m ne babbar kotun Kano za ta fara sauraren shari'ar almundaha da gwamnatin Kano ta shigar kan Ganduje.

Daga cikin wadanda ake zargi akwai Hafsat Ganduje, Umar Abdullahi Umar, da Abubakar Bawuo, Jibrilla Muhammad, kamfanin Safari Textiles da kamfanin Lesage General Enterprises.

A zaman kotu da aka yi ranar 5 Yuni, 2024, an bayar da umarnin a sada tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da sauran wadanda ake zargi da sammaci, jaridar Vanguard ta wallafa.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Yadda kururuwar mutanen Kano ya dakile yunkurin kungiyar LGBTQ

Wannan ya biyo bayan kin halartar zaman kotun da wadanda ake zargi kan tuhumar almundahanar kudin mutanen Kano su ka yi.

Kotu ta dakatar da binciken Ganduje

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya dake zamanta a Kano ta dakatar da binciken Abdullahi Ganduje da gwamnati ke yi kan zargin almundahana.

Tun da fari, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kafa kwamitin da zai binciki Ganduje bisa zargin badakalar kudin jama'a da sa hannun iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.