Sarkin Gwoza da ya tsere saboda rikicin Boko Haram ya dawo kan mulki

Sarkin Gwoza da ya tsere saboda rikicin Boko Haram ya dawo kan mulki

Mun samu labari cewa Mai martaba Sarkin Gwoza, Muhammadu Shehu Idrissa Timta, ya dawo cikin kasarsa. Hakan na zuwa ne bayan Sarkin ya shafe shekaru a waje a dalilin rikicin Boko Haram.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto dazu, Alhaji Muhammadu Shehu Idrissa Timta ya koma Garin na sa ne bayan ya yi kusan tsawon shekara 5 ya na labe a babban birnin jihar Borno watau Maiduguri.

Mai martaban ya koma gida ne a Ranar Lahadi, 14 ga Watan Yulin, 2019. Muhammadu Shehu Idrissa ya bar gida ne a 2014 lokacin da Boko Haram su ka karbe Garin Gwoza bayan sun ci kasar da yaki.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun hallaka manyan 'Yan Boko Haram

A wancan lokaci ‘yan ta’addan na Boko Haram sun kafa Daular su ta Musulunci a Garin Gwaza. Wannan ya sa Sarki Muhammadu Shehu Idrissa Timta da wasu Sarakunan Borno 4 su ka bar kasar su.

Bayan dawowar Sarkin na Gwoza, yanzu Sarakunan Dikwa da Bama watau Alhaji Muhammad Ibn Masta II El-Kanemi da kuma Alhaji Kyari Ibn Ibrahim Umar El-Kaneni ne kadai su ke gudun hijira a Borno.

Daga cikin wadanda su ka rako Sarkin gida wajen dawowa da gudun hijirar da ya yi akwai mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur da Sanata Ali Ndume da wasu manyan gwamnati.

Mai martaba Sarkin ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen rikicin na Boko Haram gaba daya inda ya ce har yanzu a na kashe jama’a a hanyar gona, har babu mai iya barin cikin Birnin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel