Aminu vs Sanusi II: An Bayyana Sahihin Sarkin Kano bayan Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara

Aminu vs Sanusi II: An Bayyana Sahihin Sarkin Kano bayan Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara

  • Kotun ɗaukaka kara mai zama a birnin tarayya Abuja ta umarci kowane ɓangare a shari'ar sarautar Kano ya koma matsayinsa na asuli
  • Da yake fashin baki kan hukuncin, Aminu Babba Ɗan'agundi ya ce kotun na nufin Aminu Ado Bayero ne halastaccen sarkin Kano
  • Ya bukaci hukumomin tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da DSS su tabbatar da an bi wannan umarni na kotu yadda ya kamata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - A yau, kotun ɗaukaka kara ta sake yin hukunci kan rigimar sarautar Kano tsakanin sarki na 15, Aminu Ado Bayero da sarki na 16, Muhammadu Sanusi II.

Kotun Daukaka Karar da ke zamanta a Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncinta na ranar 10 ga watan Janairu, wanda ya tabbatar da maida Sanusi II kan sarauta.

Kara karanta wannan

'Ba a fahimta ba': Gwamnatin Kano ta fayyace hukuncin kotu kan rigimar sarauta

Aminu Ado Bayero.
Babba Ɗan'agundi ya ce Aminu Ado ne halastaccen sarkin Kano Hoto: @HRHBayero
Asali: Facebook

A hukuncin da Mai Shari'a Okon Abang ya yanke yau Juma'a, 13 ga Maris, ya bukaci kowane ɓangare ya tsaya a matsayinsa, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko dai kotun ta soke umarnin dakatar da maida Muhammadu Sanusi II kan sarauta, kana ta umarci a maida ƙarar gaban babbar kotun Kano.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi hukunci

Amma a sababbin kararaki biyu, CA/KN/27M/2025 da CA/KN/28M/2025 da aka shigar gabanta, kotun ɗaukaka kara ta ce masu kara suna da gaskiya, ya kamata a saurari ƙorafinsu.

Kotun ta hana gwamnatin Kano aiwatar da hukuncin ranar 10 ga Janairun 2025 wanda ya amince da rushen sabbin masarautu da dawo da Sarki Sanusi II.

Bayan yanke wannan hukunci, jagoran masu kara Baffa Babba Ɗan'agundi (sarkin dawaki babba) ya ce hukuncin na nufin Aminu Ado Bayero ne sahihin Sarkin Kano.

Wanene sarkin Kano a yanzu?

Babba Ɗan'agundi ya jaddada cewa bisa la'akari da umarnin kotun ɗaukaka ƙara na cewa kowane ɓangare ya tsaya a matsayinsa na usuli, Aminu Ado ne sarkin Kano yanzu haka.

Kara karanta wannan

Rigimar sarauta ta dawo, kotu ta yi hukunci kan mayar da Sanusi II kujerarsa

A cewarsa, hukuncin ya rushe sabuwar dokar masarautar Kano 2024 da Majalisar dokoki ta yi, wacce ta dawo ta Sanusi kan sarauta kuma ta rushe masarautu biyar.

Aminu da Sanusi II.
Babba Ɗan'agundi ya ce Aminu Aso Bayero da sarakuna 4 sun koma kan sarauta bisa umarnin kotu Hoto: @HRHBayero, @MasarautarKano
Asali: Twitter

A wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin X, Ɗan'agundi ya shaidawa manema labarai a harbar kotu cewa:

"Da farko zan fara miƙa godiya ga Allah SWT, na san duk kun ji hukuncin wannan kotu mai albarka saboda a gabanku aka yi.
"Daga yau, Mai martaba sarki, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan masarautu huɗu na Kano, su ne halastattun sarakunanmu kamar yadda kotu ta ambata."
"Saboda haka ana umartar sufetan ƴan sanda na kasa, daraktan DSS da sauran hukumomin tsaro sun yi biyayya ga wannan hukunci, kotu ta ce kowa ya tsaya a matsayinsa na usuli.

- Babba Ɗan'agundi.

Kotun koli za ta warware rikicin sarauta

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar 6 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan rikicin sarautar Gwandu da ke jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Tun da farko, gwamnatin jihar Kebbi, ta roƙi kotun da ta ba su dama su ƙara gabatar da hujjoji kan buƙatar neman soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng