'Ba a Fahimta ba': Gwamnatin Kano Ta Fayyace Hukuncin Kotu kan Rigimar Sarauta
- Gwamnatin Kano ta ce hukuncin kotun daukaka kara bai soke dawo da Muhammadu Sanusi II matsayin Sarkin Kano ba
- Kwamishinan shari'a, Haruna Isa Dederi ya ce hukuncin ranar 10 ga Janairu ya tabbatar da ikon gwamnati na dawo da Sanusi kan karaga
- Kotun ta ce a ci gaba da zama a matsayin da ake ciki yanzu har sai kotun koli ta yanke hukunci kan karar da ake ci gaba da yi
- Aminu Danagundi, wanda bai gamsu da hukuncin ba, shi ya daukaka kara zuwa kotun koli yana kalubalantar dawo da Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamantin jihar Kano ta yi magana kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yi kan rigimar sarauta.
Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Haruna Isa Dederi, ya ce hukuncin kotun da ke Abuja bai soke dawo da Muhammadu Sanusi II ba.

Kara karanta wannan
Aminu vs Sanusi II: An bayyana sahihin sarkin Kano bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

Asali: UGC
Rigimar sarauta: Wane hukunci kotun ta yi?
Yayin da yake zantawa da manema labarai, Dederi ya ce hukuncin kotun daukaka kara na ranar 10 ga Janairu ya tabbatar da ikon gwamnati na dawo da Sanusi II, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan bayani na Dederi ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke kan neman dakatar da aiwatar da hukuncin da Danagundi ya shigar.
Kotun ta bayar da umarni a ci gaba da zama a matsayin da ake ciki yanzu har sai kotun koli ta yanke hukunci kan shari’ar.
A hukuncin ranar 10 ga Janairu, kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun tarayya da ya soke dawo da Sanusi II, tana mai cewa ba ta da hurumi.
Aminu Danagundi bai gamsu da wannan hukunci ba, don haka ya daukaka kara zuwa kotun koli yana kalubalantar shari’ar sarkar Kano.

Asali: Twitter
Wane martani gwamnatin Kano ta yi?
Dederi ya kara da cewa, kotun koli ce kadai ke da hurumin soke wannan hukunci na kotun daukaka kara da aka yanke a baya.
Ya jaddada cewa kotun daukaka kara ba ta soke hukuncin da ta yanke ba, sai dai ta dakatar da aiwatar da shi na dan lokaci.
Rahotanni sun ruwaito cewa alkalan kotun daukaka kara su uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Abang, sun ce bukatar dakatarwa tana da karfi.
Hakan yana nufin babu wani canji da za a yi a matsayin da ake ciki har sai kotun koli ta fitar da hukuncin karshe kan lamarin, The Guardian ta ruwaito.
Danagundi ya yi magana kan hukuncin kotu
Kun ji cewa Aminu Danagundi ya yi fashin baki kan hukuncin, Aminu Babba Ɗan'agundi ya ce kotun na nufin Aminu Ado Bayero ne halastaccen sarkin Kano.
Danagundi ya bukaci hukumomin tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da DSS su tabbatar da an bi wannan umarni na kotu yadda ya kamata.
Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun ɗaukaka kara mai zama a birnin tarayya Abuja inda ta umarci kowane ɓangare a shari'ar sarautar Kano ya koma matsayinsa na asali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng