Biyan Haraji: Majalisa Ta Yi Wa Sojoji Gata, an Gabatar da Muhimmin Kudiri a gabanta

Biyan Haraji: Majalisa Ta Yi Wa Sojoji Gata, an Gabatar da Muhimmin Kudiri a gabanta

  • Kwamitin kudi na Majalisar Wakilai ya gabatar da kuduri don cire harajin kudin shiga ga dakarun soja a Najeriya
  • Shugaban kwamitin, Abiodun Faleke ne ya bayyana haka a lokacin da ake duba dokokin haraji da Bola Tinubu ya tura
  • Faleke ya ce sun ba da shawarar a cire haraji daga albashin dakarun soja saboda muhimmancin aikin da suke yi wa kasa
  • Majalisar ta amince da shawarar kwamitin ba tare da sabani ba, domin girmama kokarin sojoji wajen kare lafiyar kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kwamitin kudi na Majalisar Wakilai ya gabatar da wani muhimmin kudiri domin mutunta kokarin sojojin Najeriya.

Kwamitin ya gabatar da kuduri na cire haraji daga albashin dakarun soja a Najeriya baki daya saboda ƙwazon da suke yi.

An gabatar da kudiri kan harajin kudin shiga na sojoji
Kwamitin majalisa ya gabatar da kudiri cire harajin kudin shiga na sojoji. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

An kara alawus na abincin sojojin Najeriya

Kara karanta wannan

An gano shugaban kasar da ya kafa kungiyar Lakurawa da yadda suka shigo Najeriya

Shugaban kwamitin, Abiodun Faleke, ne ya bayyana hakan a yau Alhamis 13 ga watan Maris, 2025, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya ƙara kuɗin ciyarwa na sojoji daga N1,500 zuwa N3,000 a kullum.

Oluyede ya kuma bayyana cewa an kaddamar da shirin gina gidaje don ba wa sojojin da ke yin ritaya wuraren zama.

An ƙaddamar da rancen sojoji da riba kashi 3% kawai, wanda ya fi sauƙi fiye da na bankuna wanda sojoji za su iya samun kayayyakin aiki da sauri.

Sabon kudiri kan haraji a majalisa

An gabatar da kudirin ne yayin nazari kai tsaye kan sabbin dokokin haraji hudu da Shugaba Bola Tinubu ya mika ga majalisar.

Wadannan kudurori na haraji na daga cikin wadanda Shugaba Bola Tinubu ya turawa majalisar tun a watan Oktoban shekarar 2024 da ta gabata.

A yayin taron, Faleke ya ce:

Kara karanta wannan

Bayan shafe shekaru ana rigimar limanci, kotu ta shiga lamarin ana azumin Ramadan

"Mai girma, kakakin majalisa da yan uwana a wannan wuri, kwamitinmu ya gabatar da kudiri kan cire haraji daga kudin shiga na dakarun sojoji.
"Wannan na daga cikin mutunta irin kokarin da suke yi a aikinsu wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya."
Majalisa ta gabatar da kudiri da ya shafi biyan harajin sojoji
Kwamitin majalisa ta gabatar da kudirin don cire haraji kan kudin shiga na dakarun sojoji. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Matsayar mafi yawan 'yan majalisa kan kudirin

Kamar yadda labarin ya nuna, kwamitin ya dauki matakin ne saboda irin rawar da dakarun soja ke takawa wajen kare tsaron kasar nan.

Wannan shawara ta kwamitin ta samu amincewar dukkan ‘yan majalisar ba tare da wata gardama ko rashin jituwa ba.

Cikakken bayani kan wannan batu zai zo nan gaba yayin da majalisar ke ci gaba da aiki kan dokokin haraji na kasa.

Majalisa za ta yi zama kan kudirin haraji

Mun ba ku labarin cewa Majalisar wakilai za ta yi nazari daga sashe zuwa sashe kan rahotannin kudirin gyaran haraji da kwamitin sauraron ra’ayoyin jama’a ya tattaro.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta zauna kan kudirin harajin Tinubu kafin amincewa da shi

Shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya bukaci dukkan ‘yan majalisar su kasance a wurin domin tabbatar da cewa an duba ra'ayoyin yadda ya dace.

Daga cikin kudirin dokar da aka gabatar akwai soke dokar kafa hukumar tattara haraji ta kasa, sannan a kirkiri wata sabuwa da ikon majalisa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng