'Ba Alheri ba ne': ASUU Ta Gano Bala'in da Gyaran Harajin Tinubu Zai Jawo wa Ilimi

'Ba Alheri ba ne': ASUU Ta Gano Bala'in da Gyaran Harajin Tinubu Zai Jawo wa Ilimi

  • Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta ce dokar sauya haraji za ta lalata ilimi daga 2030, wanda zai haifar da koma baya ga harkar
  • Legit Hausa ta rahoto cewa asusun TETFund ya na taimaka wa jami’o’i da kudin gudanarwa, bincike da kuma gine-gine
  • Gwamnatin Bola Tinubu dai ta ware kashi 7 ga ilimi a kasafin kudin 2025, wanda ASUU take kallo a matsayin "nuna rashin fifiko"

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benin - Kungiyar ASUU reshen Benin ta yi watsi da kudirin dokar sauya haraji ta Najeriya, tana cewa zai lalata jami’o’in gwamnati.

A wata ganawa da manema labarai, mai kula da yankin ASUU a Benin, Farfesa Monday Igbafen, ya ce dokar za ta kashe ilimi a Najeriya.

Kungiyar ASUU ta gargadi gwamnatin Tinubu kan aiwatar da kudurorin gyaran haraji.
Kungiyar ASUU ta nunawa gwamnatin Tinubu cewa babu alkairi a gyaran haraji. Hoto: @asuunews, @officialABAT
Asali: Facebook

ASUU ta gargadi gwamnati kan lalata TETFUND

Kara karanta wannan

An sanya lokacin da maniyyata za su kammala biyan kudin Hajjin 2025 a jihar Kwara

Farfesa Monday Igbafen ya ce sashe na 59(3) na dokar zai rage kason kudin da ake warewa asusun TETFund zuwa kashi 50 a shekarar 2025, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudurin dokar zai sa asusun TETFund ya rage samun kudi zuwa kashi 66 a shekarun 2027 zuwa 2029, sannan kasafinta ya tsaya cak daga shekarar 2030.

Kungiyar ASUU ta ce ilimi dukiyar jama’a ce, don haka bai kamata gwamnati ta kashe ilimi ta hanyar wannan dokar haraji ba.

Kungiyar ASUU ta zargi gwamnati da shirin lalata ilimi

Kungiyar malaman ta bayyana cewa dokar na barazana ga cigaban TETFund da ke tallafa wa ci gaban jami’o’i da horar da ma’aikata.

ASUU ta ce TETFund ginshiki ne wajen cigaban jami’o’i, tun kafuwarsa yana tallafa wa horar da malamai, gine-gine da bincike a Najeriya.

Farfesa Igbafen ya ce har yanzu gwamnati ba ta warware matsalolin da suka taso daga yarjejeniyar ASUU ta 2009 ba.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi yadda aka zuba jarin $6.7bn a bangaren makamashi

ASUU ta fadi illar durkushewar TETFUND

Ya kara da cewa “mutuwar” TETFund daga shekarar 2030 za ta jefa ilimin Najeriya cikin halin ha'ula'i.

Kungiyar ta ce soke TETFund zai dakile cigaban jami’o’i, ya kuma jawo Najeriya ta zama butal a jerin kasashe masu ilimi na duniya.

Ta bukaci ‘yan Najeriya da su tashi tsaye don dakile wannan barazana ga ilimi da cigaban jami’o’i.

ASUU ta caccaki Tinubu kan kasafin 2025

ASUU ta yadda cewa kaso tsakanin kashi 5 zuwa 7 na kasafin shekara shekara da gwamnatin Najeriya ke warewa ilimi yana barazana ga cigaban kasar nan.

Farfesan ya buga misali da cewa ware kashi 7 cikin 100 na kasafin 2025 ga ilimi da gwamnatin Bola Tinubu ta yi bai dace ba.

Kungiyar ta ce tana nan daram akan matsayar cewa TETFund ta ci gaba da zama ginshiki ga cigaban ilimi a Najeriya.

Gwamnoni 36 sun amince da gyaran haraji

Kara karanta wannan

2027: Tsofaffin gwamnnonin PDP 5 da za su iya goyon bayan Tinubu idan ya nemi tazarce

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin Najeriya 36 sun amince da bukatar shugaba Bola Tinubu ta gyaran haraji da tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai kuma gwamnonin kasar sun gabatar da sabon tsarin rabon harajin VAT ga gwamnatin Tinubu matsayin sharadinta na amincewa da gyaran harajin.

Kungiyoyin gwamnonin (NGF) ta ce sabon tsarin zai magance damuwar gwamnoni game da dokar sauya haraji da shugaban kasar ya kawo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.