Ministan Tinubu Ya Caccaki El Rufai kan Sukar gwamnatin APC, Ya Lissafo Laifukansa a Kaduna

Ministan Tinubu Ya Caccaki El Rufai kan Sukar gwamnatin APC, Ya Lissafo Laifukansa a Kaduna

  • Yusuf Abdullahi Ata bai ji daɗin sukar da Nasir El-Rufai ya yi wa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba
  • Ƙaramin ministan na gidaje da ci gaban birane ya bayyana cewa har yanzu El-Rufai na jin haushi ne saboda bai samu muƙami ba
  • Ya nuna gwamnatin Shugaba Tinubu za ta ci gaba da maida hankali wajen cika alƙawuran da ta ɗaukarwa ƴan Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi wa Nasir El-Rufai martani kan sukar gwamnatin APC.

Ƙaramin ministan ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta ci gaba da maida hankali kan cika alƙawuran da ta ɗauka, duk da wasan kwaikwayon da Nasir El-Rufai ke yi.

Yusuf Abdullahi Ata ya caccaki El-Rufai
Yusuf Abdullahi Ata ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu Hoto: Nasir El-Rufai, Yusuf Abdullahi Ata
Asali: Facebook

Yusuf Abdullahi Ata ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka kan harkokin yaɗa labarai, Seyi Olorunsola ya fitar, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

El Rufai ya bayyana alfarmar da Tinubu ya nema a wajensa gaban duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tinubu ya caccaki El-Rufai

Ministan ya bayyana cewa fushin da El-Rufai ke yi da jam’iyyar APC ya samo asali ne daga gazawarsa wajen samun muƙamin minista a gwamnatin Tinubu.

Ya bayyana cewa an hana El-Rufai muƙamin minista ne saboda bai tsallake tantancewar tsaro ba.

A cewar Ata, suka da zargin da El-Rufai ke yi wa gwamnatin Tinubu, har da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar SDP, alamu ne na ɗan siyasar da aka kusa mantawa da tarihinsa.

"Lokacin da yake a matsayin ministan Abuja a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo ya kawo manufofi masu cece-kuce da salon jagoranci mai tsauri."
“Wannan hali ya ci gaba da bibiyarsa a tafiyarsa ta siyasa, tun daga lokacin da yake adawa da shekarun farko na kafuwar APC har zuwa mulkinsa na wa’adi biyu a matsayin gwamnan jihar Kaduna."
“Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa a wannan lokacin, yayin da Shugaba Tinubu ke maida hankali kan magance matsalolin da suka dabaibaye Najeriya, El-Rufai ya zaɓi ɗana sabon tarkon siyasa.”

Kara karanta wannan

"Na san waɗanda suka biya kuɗi kafin a naɗa su minista," El Rufai ya tona asiri

- Yusuf Abdullahi Ata

Ata ya jefi El-Rufai da gazawa kan tsaro a Kaduna

Ata ya jaddada cewa a lokacin da El-Rufai ke gwamna, jihar Kaduna ta fuskanci matsalar tsaro da ba a taɓa gani ba, inda rikicin ƙabilanci da na addini suka jawo asarar rayuka.

"A ƙarƙashin jagorancinsa, Kaduna ta zama daya daga cikin jihohin da suka fi yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon rikice-rikice da hare-haren ƴan ta’adda."
"Abin da ya fi shahara shi ne yadda ya taɓa bayyana cewa ya biya wasu ƴan bindiga kuɗade, maganar da har yanzu ke yi masa tabo a tarihinsa da ayar tambaya kan rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."
"Salon jagorancinsa ya sha suka saboda yadda ya raba kawunan jama’a, tare da aiwatar da manufofi da suka ware ƙananan ƙabilu da ƙara rura wutar rikice-rikice a jihar."

- Yusuf Abdullahi Ata

El-Rufai ya tabo batun rasa muƙami a gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

El Rufai ya bayyana yadda suka yi da Buhari kan batun ficewarsa daga APC zuwa SDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bai fice daga jam'iyyar APC ba, saboda ya rasa muƙamin minista.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tun da farko, shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya nemi ya zo ya yi aiki a gwamnatinsa, domin ya ba da tasa gudunmawar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng