El Rufai Ya Bayyana Alfarmar da Tinubu Ya Nema wajensa gaban Duniya

El Rufai Ya Bayyana Alfarmar da Tinubu Ya Nema wajensa gaban Duniya

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya ce ko kaɗan bai nemi muƙami ba a gwamnatin shugaba Bola Tinubu
  • Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Shugaban kasa Tinubu ne da kansa ya nemi ya zo ya ba da tasa irin gudunmawar a gwamnatinsa
  • Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce ƙin samun muƙamin minista ba shi daga cikin dalilansa na ficewa daga jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce bai taɓa neman muƙamin minista a gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba.

Nasir El-Rufai ya ce duk da cewa ya halarci tantancewa a majalisa, ya yi hakan ne saboda shugaban ƙasa da kansa ya roƙe shi kan ya zo ya yi aiki a gwamnatinsa.

El-Rufai ya ce bai nemi mukami a gwamnatin Tinubu ba
El-Rufai ya ce Tinubu ne ya nemi ya yi aiki a gwamnatinsa Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da jaridar BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya soki El Rufai kan sukar gwamnatin APC, ya fadi laifukansa a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya roƙi alfarma wajen El-Rufai

Nasir El-Rufai ya ce shugabaTinubu ya roƙe shi da ya taimaka wajen cimma burinsa na samar da ingantacciyar wutar lantarki a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa ƙin ba shi muƙamin minista, ba shi ba ne dalilin da ya sa ya fice daga jam'iyyar APC.

"Wasu na tunanin na fice ne saboda ba a naɗa ni minista ba, amma ban taɓa neman wannan muƙamin ba. Na je tantancewa ne saboda shugaban ƙasa ya roƙe ni da na yi aiki tare da shi."
"Ya zo wurina a Kaduna, muka tattauna kan burinsa na samar da ingantacciyar wutar lantarki, kuma ya nemi na taimaka masa wajen cimma hakan. A wancan lokaci, na yi tunanin da gaske yake yi."

- Nasir El-Rufai

Wane da-na-sani El-Rufai ya yi kan Tinubu?

Ya kuma yi watsi da jita-jitar da ke cewa ficewarsa daga APC ta samo asali saboda kasa cika masa wata buƙata da ya ke da ita a gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

"Na san waɗanda suka biya kuɗi kafin a naɗa su minista," El Rufai ya tona asiri

“Ba na da-na-sanin goyon bayansa, amma na ji takaici. Dalilin da ya sa ban yi nadama ba kuwa shi ne saboda abubuwa guda biyu."
"Na farko, shugabannin Yarbawa daga Kudu maso Yamma sun zo wurina a Kaduna, sun bayyana min cewa ƴan siyasa Musulmi a yankinsu na fuskantar matsaloli. Wannan ne ya sa na marawa Tinubu baya."
“Abu na biyu kuma, mun yi yarjejeniya cewa a 2023, mulki ya koma Kudu don tabbatar da adalci da daidaito a ƙasa."

- Nasir El-Rufai

Nasir El-Rufai ya caccaki APC

El-Rufai ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar da ta yi watsi da manufofin da aka kafa ta a kai, a yanzu ta fi mayar da hankali kan moriyar wasu ƴan tsiraru maimakon hidimtawa al’umma.

“APC ta watsar da jama’a. Kowa yana yin son zuciyarsa da tara kuɗi. Gwamnati ta koma kasuwanci, inda komai ke da farashi. Babu adalci."
"Duk muƙamin da za a ba da, suna zaɓan mutanen Legas ne kawai. Jam’iyyar ta mutu. Wannan ne ya sa na tuntuɓi Tunde Bakare, Buhari, Abdullahi Adamu, Adams Oshiomhole, da Bisi Akande kafin na yanke shawara."

Kara karanta wannan

El Rufai ya bayyana yadda suka yi da Buhari kan batun ficewarsa daga APC zuwa SDP

- Nasir El-Rufai

Jam'iyyar NNPP ta ba El-Rufai wa'adi

A wani labarin kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi martani mai zafi ga Nasir El-Rufai kan zargin da ya yi na cewa gwamnatin APC na da hannu a rikicin da take fama da shi.

Jam'iyyar NNPP ta ba tsohon gwamnan na jihar Kaduna wa'adi ya janye kalamansa tare da ba da haƙuri, ko ta ɗauki matakin shari'a a kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng