Gwamna Buni Ya Koka kan Rashin Bayyana Nasarorinsa, Ya Gano Dalili

Gwamna Buni Ya Koka kan Rashin Bayyana Nasarorinsa, Ya Gano Dalili

  • Gwamnan jihar Yobe ya koka kan yadda nasarorin da ya samu a gwamnatinsa ba a bayyana su ga al'umma
  • Mai Mala Buni ya koka da cewa kafafen yaɗa labarai ba su kawo rahotanni yadda ya kamata kan nasarorin da ya samu a cikin shekaru biyar da suka gabata
  • Ya nuna cewa ya samu nasarori a fannoni daban-daban amma ba a kawo rahotanninsu yadda ya kamata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana damuwarsa kan yadda kafafen yaɗa labarai ba su kawo rahotannin nasarorinsa.

Gwamna Mai Mala Buni ya koka da cewa kafafen yaɗa labarai ba su ba da cikakken rahoto kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Gwamna Buni ya koka
Gwamnan Yobe ya ce ba a bayyana nasarorinsa Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin buɗe taron bita na kwanaki uku da ma’aikatar harkokin cikin da al’adu ta shiryawa jami’an yaɗa labarai a Damaturu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bayan an nemi ya fice daga PDP, gwamna ya ɗauko mutum 8 ya ba su muƙamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mai Mala Buni ya yi ƙorafi

Gwamna Buni ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Baba Malam Wali, a wajen taron.

Ya bayyana cewa jihar Yobe na daga cikin jihohin da kafafen yada labarai ba su kawo rahotanni a kansu, saboda gazawar hukumomin gwamnati wajen bayar da bayanai kan nasarorin da suka samu.

Ya koka da cewa gwamnatinsa ta cimma manyan nasarori a fannonin tsaro, kiwon lafiya, ilimi, noma, da kuma samarwa matasa da mata abin yi, amma waɗannan nasarorin ba a bayyana su sosai ba.

Gwamnan ya jaddada buƙatar jami’an yaɗa labarai na ma’aikatu da hukumomin jihar su haɗa kai da kafafen yaɗa labarai don yaɗa shirye-shiryen gwamnatinsa da nasarorin da ta samu, tare da isar da manufofin gwamnati ga al’ummar jihar.

Gwamna Buni ya shirya ɗaukar mataki

Mai Mala Buni ya ce gwamnatinsa ta duƙufa wajen ba ma’aikatan gwamnati kayan aiki da horaswar da ake buƙata domin fuskantar ƙalubalen da zamani ya zo da su wajen isar da saƙo ga jama’a.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi ɓaram ɓarama a siyasar APC, ya saki layi a gaban Ganduje

Buni ya kuma bayyana muhimmancin yaɗa labarai a matsayin hanyar da za ta taimaka wajen inganta dangantaka tsakanin gwamnati da al’umma.

Ya yi kira ga jami’an yaɗa labarai da su kasance masu nuna ƙwarewa da kwazo wajen sauke nauyin da ke kansu.

Ya ƙara da cewa idan babu isasshen rahoto kan abin da gwamnati ke yi, al’umma ba za su fahimci irin jajircewar da take yi ba wajen kawo ci gaba a fannoni daban-daban ba.

Ya ce horon da aka shirya zai taimaka wajen bunƙasa ƙwarewar jami’an yaɗa labarai a fannin sadarwa, musamman wajen amfani da sababbin hanyoyin sadarwa da fasahohin zamani don isar da saƙo ga al’umma.

Gwamna Buni ya ƙirƙiro sabuwar ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ƙirƙiro sabuwar ma'aikatar kula da harkokin kiwon dabbobi.

Bayan ƙirƙiro sabuwar ma'aikatar, Gwamna Buni ya buƙaci sakatare gwamnatin jigar (SSG) da shugaban ma'aikatan jihar su tsara yadda ayyukan ma'aikatar za su kasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng