Gwamnan Yobe Ya Tsaya a Hanya, Ya Raba Kudi ga Talakawa Masu Saran Itace a Daji

Gwamnan Yobe Ya Tsaya a Hanya, Ya Raba Kudi ga Talakawa Masu Saran Itace a Daji

  • Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya yi ziyarar bazata a aikin hanyar Damaturu-Kalallawa, inda ya tallafa wa ma’aikata da wasu talakawa
  • Musa Mai Itace da wasu masu itace sun samu tallafi daga gwamnan, har Musa ya bayyana cewa ya ga Lailatul Kadir da ya hadu da gwamna
  • Al’umma da dama sun yi ta yabon gwamnan a kafar sada zumunta saboda aikin alherinsa ga talakawan yayin da ya fita duba aikin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Mai girma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya gudanar da ziyarar bazata wajen aikin hanyar Damaturu zuwa Kalallawa.

A yayin wannan ziyara, gwamnan ya yi ta tallafa wa talakawa da ma’aikata tare da tabbatar da ci gaban aikin.

Mai Mala
Gwamnan Yobe ya tallafawa talakawa. Hoto: Mamman Mohammed
Asali: Facebook

Legit ta tattaro yadda lamarin ya faru ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin Yobe, Mamman Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya jawo farin ciki ga ma’aikatan hanya, masu itace, da matafiya, inda suka rika yi wa gwamnan addu’o’i da fatan alheri.

Gwamnan Buni ya tallafa wa masu itace

A lokacin da gwamna Mai Mala Buni ya tsaya a wasu wurare a hanya, ya lura da wasu bayin Allah da ke tura itace daga daji zuwa cikin garin Damaturu.

Biyo bayan hakan, gwamnan ya umurci daya daga cikin hadimansa ya ba su tallafin kudi domin rage musu radadin rayuwa.

Musa Mai Itace, wanda ya karɓi kyautar N50,000, ya nuna farin cikinsa sosai, yana cewa;

“Alhamdulillah yau na sadu da Lailatul Kadir. Na ga gwamna kuma na samu kyauta mai tsoka. Allah ya tsare mana Gwamna Buni, amin.”

Haka kuma, wani mai itace, Tanko, ya bayyana farin cikinsa, yana mai cewa,

“Ashe yau Allah zai sada ni da wannan dama. Na gode wa Allah, na gode Gwamna Mai Mala Buni.”

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su

Tanko mai itace ya bayyana cewa bai tashi da niyyar zuwa itace ba amma kaddara ta dauko shi saboda Allah ya nufi zai samu kyautar.

Tallafi ga ma’aikatan hanya da matafiya

Baya ga masu itace, gwamna ya kuma tallafa wa ma’aikatan da ke aikin hanyar Damaturu-Kalallawa.

A duk inda ya tsaya duba aikin, gwamna ya ba ma’aikatan tallafi domin kara musu kwarin gwiwa.

Matafiya a motocin fasinja suma ba a barsu a baya ba, domin sun tsaya sun karɓi tallafin gwamna Mai Mala Buni.

Lamarin ya kara jawo farin ciki a zukatan jama’a, inda wasu suka bayyana cewa gwamnan ya cancanci yabo saboda taimakon al’umma.

Yabon jama’a a kafar sada zumunta

Bayan da labarin ya bazu a kafar sada zumunta, mutane da dama sun yi ta yabon Gwamna Mai Mala Buni bisa wannan aikin alheri.

Wasu sun bayyana cewa irin wannan shugabanci ne ke kawo ci gaban kasa da jin dadin al’umma.

Kara karanta wannan

Mukaila Senwele: Fitaccen mawakin Najeriya daga Arewa ya rasu, an yi masa sutura

A nasu bangaren, masu itace da ma’aikatan hanya sun rika yi wa gwamnan addu’a, suna rokon Allah ya kara masa lafiya da nasara.

Tinubu zai raba tallafin kudi ga talakawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fitar da shiri na musamman domin tallafawa talakawan Najeriya.

A karkashin shirin, ana sa ran cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tallafawa 'yan Najeriya miliyan 70 da kudi N75,000 domin rage fatara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng