Ta Faru Ta Kare: Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Sahihancin Zaben Gwamnan APC

Ta Faru Ta Kare: Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Sahihancin Zaben Gwamnan APC

  • Kotun Koli ta yi zama kan shari'ar da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Agboola Ajayi ya shigar kan zaben jihar Ondo
  • Alkalai sun bayyana cewa Ajayi ba shi da hurumin shigar da kara kan harkar jam'iyyar APC saboda shi 'dan PDP ne
  • Kotun ta tabbatar da cewa karar ta zama ba ta da amfani saboda wa'adin kwana 14 da doka ta tanada ya wuce tun da farko
  • Kotun ta umarci Ajayi ya biya N2m ga kowanne daga cikin wadanda ake kara guda hudu kan zaben jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta Najeriya ta yi watsi da karar da dan takarar gwamnan Ondo, Agboola Ajayi na PDP ya shigar kan takarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC.

Kara karanta wannan

Jagoran PDP ya shiga fargaba, ya hango yadda jam'iyyarsa ke neman fadawa hannun APC

A hukuncin da mai shari’a Lawal Garba ya jagoranta, kotun ta ce an shigar da karar bayan wa'adin doka kan korafin ya wuce kuma Ajayi ba shi da hurumi.

Kotu ta raba gardama kan shari'ar zaben Ondo
Kotun Koli ta kori karar PDP inda ta tabbatar da nasarar APC a zaben Ondo. Hoto: Ajayi Agboola, Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Korafin dan takarar PDP a zaben Ondo

Kotun ta bayyana cewa karar ta shafi harkokin cikin gida ne na jam’iyyar APC, ba hurumin wata jam’iyya ce ta tsoma baki ba, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajayi ya kai kara Kotun Tarayya a Abuja a ranar 7 ga Yuni, 2024, ya na kalubalantar takarar Aiyedatiwa bisa matsalar cancantar mataimakinsa.

Bayan korafin wadanda ake kara, Babban Alkalin Tarayya ya mayar da shari’ar zuwa kotun tarayya da ke Akure.

A ranar 2 ga Disamba, 2024, Mai shari’a T.B. Adegoke ya yi watsi da karar, yana cewa ba a shigar da ita daidai tsarin doka ba.

Kotun ta ce tun da Ajayi ya zargi Adelami da laifin jabun takardu da rantsuwar karya, ya kamata ya bi hanyar da ta dace.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya karbi bakuncin kungiyar 'Obedient' a Kano, ya ba su shawarwari

Ajayi bai gamsu da hukuncin Kotun Tarayya ba, don haka ya daukaka kara zuwa Kotun daukaka kara a sashen Akure.

Kotu ta kori karar PDP a shari'ar zaben Ondo
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa a Ondo. Hoto: Lucky Aiyedatiwa, Ajayi Agboola.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotu ta yi kan zaben Ondo?

Kotun ta ce masu shigar da karar ba su da ikon bin wannan kara, hakan ya sa karar ba ta da inganci, cewar rahoton Punch.

Haka kuma, kotun ta tabbatar da cewa karar ta haramta saboda an shigar da ita bayan wa'adin da doka ta kayyade ya kare.

Kotun ta jaddada cewa lamarin ya fara ne a ranar 20 ga Mayu, 2024, lokacin da aka mikawa INEC fom din takara.

Sai dai masu kara sun kai kara kotu a ranar 7 ga Yuni, 2024, bayan wa’adin kwanaki 14 da doka ta tanada.

Saboda haka, kotun ta yi watsi da karar tare da umartar Ajayi ya biya N2m ga kowane daga cikin wadanda ake kara guda hudu.

Gwamna ya ware makudan kudi saboda WAEC

Kara karanta wannan

'Asara ne': Dillalan mai sun koka kan rage farashin fetur, sun kawo mafita mai ɗorewa

Kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, zai kashe N634m domin biyan kudin jarabawar WASSCE ga daliban makarantun gwamnati.

Sanarwar gwamnatin jihar Ondo ta bayyana cewa dalibai 23,048 da suka ci jarabawar karin girma ta JSS II ne za su ci gajiyar shirin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng