Matasa Sun Fusata a Watan Azumi, Sun Ƙona Fadar Mai Martaba Sarki a Arewacin Najeriya
- Zanga-zanga ta ɓarke a yankin ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benuwai, matasa sun ƙona fadar sarki da sakatariya
- Rahotanni sun bayyana cwwa kisan da wasu ƴan bindiga suka yi wa dakarun rundunar ƴan sa-kai ne ya harzuka mutanen yankin
- Shugaban ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma ya tabbatar da faruwar lamarin, ana zargin wasu ƴan daba ne suka shiga cikin masu zanga-zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Fusatattun matasa sun ɓarke da zanga-zanga mai haɗe da tashe-tashen hankula a yankin karamar hukumar Gwer ta Yamma da ke jihar Benuwai.
Masu zanga-zangar sun ƙone sakateriyar ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma da kuma fadar sarkin Naka, Ter Nagi, Cif Daniel Abomtse.

Asali: Original
Me ya haddasa zanga-zangar matasa?
Jaridar Daily Trust ta tataro cewa matasan sun aikata wannan ɓarna ne sakamakon kisan wasu jami’an tsaron al’umma watau ƴan sa'kai guda uku a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun kuma banka wa wani otal da ake zargin mallakin Sanata Titus Zam ne wuta a Naka, hedikwatar ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa tashin hankalin ya fara ne da safiyar Talata, yayin da matasa suka kawo gawarwakin ƴan sa'kai da da ’yan bindiga suka kashe.
Kashe jami'an tsaro ya harzuƙa mutane
Ya ce ƴan ta'adda sun hallaka jami'an tsaron su uku a ranar Litinin da dare a wani ƙauye da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma.
“Matasan sun fusata ne ne saboda ’yan bindiga na kashe mutanenmu amma gwamnatin jiha ba ta ɗaukar wani mataki.
"Tun da aka kawo gawarwakin jami’an tsaron da safe, matasa suka ɓarke da zanga-zanga, suka ƙone sakateriyar ƙaramar hukuma, fadar Ter Nagi da wani otal da ake cewa ta Sanata Titus Zam ne,"

Kara karanta wannan
Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa
- In ji shi.
Shugaban ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma, Victor Ormin, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa matasa ne suka fara zanga-zanga don nuna fushinsu kan kisan.
Ƴan daba sun shiga cikin zanga-zanga
Sai dai ya ce daga bisani wasu ɓata gari suka yi amfani da damar, suka saje da matasan, suka yi wannan ƙone-ƙone.
“Eh, sun ƙone sakateriya da fadar Ter Naka. Ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaro uku ne a ƙauyen Garuwa.
"Da aka kawo gawarwakinsu Naka, sai matasa suka fara zanga-zanga, daga nan kuma wasu ’yan daba suka ƙwace damar suka fara lalata dukiyoyi,”
- In ji shi.
Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Catherine Anene, ba ta amsa kira ko fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Mata sun yi zanga-zanga a Benuwai
A baya, kun ji cewa mata a garin Jato Aka da ke karamar hukumar Kwande a jihar Benuwai sun yi zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga kan manoma.
An tattaro cewa matan sun gudanar da wannan zanga-zanga ne domin nuna ɓacin ransu kan yawan kashe-kashen rayukan da ake yi a yankin ƴan kwanakin nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng