'Babu Dole a Addini': Gwamna Ya Hana Wa'azi a Bainar Jama'a, Ya Fadi Tarar da Za a Biya

'Babu Dole a Addini': Gwamna Ya Hana Wa'azi a Bainar Jama'a, Ya Fadi Tarar da Za a Biya

  • Gwamna Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya hana wa’azi da lasifika a kasuwanni, yana mai cewa hayaniya na hana mutane sukuni
  • A wani bidiyo da ya yadu, an ga Soludo yana dakatar da wani mai wa’azi a kasuwa, yana umurtarsa da ya guji tayar da hayaniya a wajen
  • Tsohon gwamnan CBN ya bayyana cewa duk wanda ya karya dokar zai biya tarar N500,000, ya ba da shawara a yi wa’azi a coci ko wasu wurare
  • Farfesan ya jaddada cewa kasuwa ba coci ba ce, mutane sun zo ciniki, don haka ba daidai ba ne a tilasta musu jin wa’azi a irin wannan wuri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya gargadi masu yin wa’azi a lasifika a wuraren taruwar jama'a.

Kara karanta wannan

Yadda wani matashi ya kashe 'Admin' saboda an cire shi a dandalin WhatsApp

Gwamnan yana magana musamman ga masu wa'azi a kasuwanni, yana mai cewa hakan na haddasa hayaniya da matsala ga jama’a.

Gwamna ya haramta yin wa'azi a kasuwanni
Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya hana yin wa'azi a bainar jama'a. Hoto: Charles Chukwuma Soludo.
Asali: Facebook

Gwamna ya karyata labarin kama mata a jiharsa

A wani bidiyo da ya yadu a dandalin X wanda Tribune ta gani ranar Asabar, an ga Soludo yana dakatar da wani mai wa’azi a kasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan yada wani labari cewa Gwamna Soludo zai fara cafke masu yawo babu rigar nono a jihar.

Sai dai Gwamnatin Anambra ta karyata jita-jitar kama mata da ba su saka rigar nono da dan kamfai a wuraren taruwar jama'a.

An yada wani bidiyo a kafafen sada zumunta cewa Gwamna Soludo ne ya ba da umarnin kama matan.

Mai magana da yawun gwamnan ya ce labarin karya ne, mai cike da shiririta, kuma gwamnati ba ta tsoma baki a zaben tufafin jama'a ba.

Gwamna ya fadi tarar da masu yin wa'azi a kasuwa za su biya
Gwamna Charles Soludo ya haramta yin wa'azi a cikin jama'a ko kasuwanni. Hoto: Charles Chukwuma Soludo.
Asali: Facebook

Gwamna ya hana Fasto yin wa'azi a kasuwa

Kara karanta wannan

Ramadan: Direba ya murkushe sufetan ɗan sanda da ke bakin aiki a masallacin Abuja

A cikin faifan bidiyon da Chijioke Eruchalu ya wallafa a X, Soludo ya umurci mai wa'azi da ya guji tayar da hayaniya maimakon haka ya je coci.

Tsohon gwamnan CBN ya bayyana cewa duk wanda ya karya dokar gurbatar sauti zai fuskanci tarar N500,000.

Ya ce:

"Idan kana son yin wa’azi, ka tafi coci, ba za ka zo kasuwa ka tilasta wa mutane jin wa’azinka ba, Idan mutum yana so, zai je cocinka."
"Ya kamata a kama ka don karya doka, Dole ne mu kare ‘yancin kowa, amma ba za ka iya canza kasuwa zuwa coci ba."
"Za mu tilasta ka biyan N500,000 don amfani da wannan fili, Ba za mu yarda da irin wannan ba."

Gwamna ya tona masu taimakawa yan bindiga

Kun ji cewa Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya gano yadda bokaye da malaman tsibbu ke yaudarar matasa suna shiga harkokin laifi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu taron siyasa a Najeriya, an harbi mutane 14

Soludo ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakan shawo kan wannan matsala kuma tuni ta fara bincike kan bokaye da irin waɗannan malamai.

Daga cikin laifukan da bokayen ke yaudarar matasa su fara har da safarar miyagun kwayoyi da shiga kungiyoyin ƴan bindiga da garkuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng