Yadda Wani Matashi Ya Kashe 'Admin' Saboda an Cire Shi a Dandalin WhatsApp

Yadda Wani Matashi Ya Kashe 'Admin' Saboda an Cire Shi a Dandalin WhatsApp

  • An kama wani mutum da aka ruwaito ya hallaka abokinsa bayan da aka cire shi a wani dandalin WhatsApp, lamarin da ya jawo bacin rai a tsakaninsu
  • A bangare guda, wasu tsageru sun yi kutse ga WhatsApp din minista a Najeriya, inda ya bayyana yanayin da ya shiga kan wannan lamari
  • Ba sabon lamari bane a sami aukuwar irin wadannan abubuwa masu daga hankali, musamman a tsakanin matasa da ke amfani da kafafen sada zumunta

Peshawar, Pakistan - Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a birnin Peshawar, babban birnin yankin Khyber Pakhtunkhwa a kasar Pakistan, inda wani mutum ya harbe 'admin', wato mai kula da dandalinsu na WhatsApp har lahira.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wanda aka kashe, mai suna Mushtaq Ahmed, shi ne ke da alhakin tafiyar da dandalin na WhatsApp, kuma an gano cewa ya cire wani mutum mai suna Ashfaq daga ciki, lamarin da ya haddasa rikici tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

Bayan faruwar wannan al’amari, dangin Ahmed sun yi kokarin sasanta su ta hanyar shirya wata tattaunawa domin warware matsalar.

Yadda matashi ya yi barna kan abokinsa
An kama wani matashi bisa kisa na cire a dandalin WhatsApp | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Sai dai, yayin da aka hadu domin yin sulhu, Ashfaq ya bayyana dauke da bindiga inda ya bude wuta kan Ahmed har lahira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa Ashfaq ya kashe Ahmed?

Rahoton ‘yan sanda ya bayyana cewa bayan cire Ashfaq daga dandalin na WhatsApp, ya fusata sosai. Dan uwansa ya ce Ashfaq ya kasa hakura da cire shi, lamarin da ya sa ya dauki doka a hannunsa.

A cewar rahoton Channels TV, dan uwan Ahmed ya ce sun yi kokarin sulhu da Ashfaq, amma duk da haka ya zo taron dauke da makami. Da haduwarsu, sai kawai ya harbe Ahmed har lahira, ba tare da bata lokaci ba.

‘Yan sanda sun tabbatar da cewa Ashfaq ya aikata kisan ne a matsayin martani ga cire shi daga dandalin WhatsApp.

Wannan lamari na daya daga cikin irin tashin hankalin da ke yawaita a wannan yanki saboda rashin ingantaccen tsarin shari’a, yawaitar makamai da kuma tasirin al’adun gargajiya na yankin.

Kara karanta wannan

Ramadan: Direba ya murkushe sufetan ɗan sanda da ke bakin aiki a masallacin Abuja

Sakon gwamnatin Najeriya kan satar bayanai a WhatsApp

A wani labari makamancin haka, Ministan Ilimi na Najeriya, Farfesa Tahir Mamman, ya sanar da cewa an kutsa masa kai a lambar wayarsa da yake amfani da ita a WhatsApp.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ministan ya gargadi jama’a da su guji karbar kira ko amsa sakonni daga lambarsa da aka yi kutse. Ya ce ana amfani da ita ba bisa ka’ida ba.

Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta tabbatar da wannan kutse, inda ta nemi jama’a da su yi hattara da duk wani sako da ke bukatar taimako daga lambar. Hukumomin tsaro sun fara bincike kan lamarin domin gano wadanda ke da alhakin kutse din.

An kama wani da ake zargi da sata a MTN

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa an kama wani mutum da ake zargi da kutse a shafin MTN. Sai dai, rahoton da ya yadu cewa masu kutse sun share bashin da MTN ke bin wasu kwastomomi ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu taron siyasa a Najeriya, an harbi mutane 14

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Update King ya yada labarin da ke nuna cewa wani matashi mai shekara 23, Jeffrey Okafor, ya kutsa shafin MTN.

Amma bincike ya nuna cewa wannan mutumin ba shi ne ya aikata laifin ba, kuma MTN ta bayyana cewa matsalar da ta faru sakamakon wani tsarin fasaha ba kutse ba.

Hukumomi sun shawarci jama’a da su daina yarda da jita-jita da ba su da tushe kuma su rika tantance gaskiyar labarai kafin yada su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.