ICPC na Zargin Wasu Tsofaffin Ma'aikatan El Rufai Sun Saci N64m, Za a Shiga Kotu
- Hukumar ICPC za ta gurfanar da wasu tsoffin mukarraban gwamnatin Nasiru El-Rufai kan zarginn karkatar da Naira miliyan 64
- ICPC ta zargi Lawal Adebisi da sauran mutanen da almundahanar kudi ta hanyar amfani da kamfanin Solar Life Nigeria Limited
- Majalisar dokokin Kaduna ta ce gwamnatin El-Rufai ta wawure Naira biliyan 423, amma tsohon gwamnan ya musanta zargin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Hukumar ICPC za ta gurfanar da wasu tsoffin mukarraban tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai, kan zargin almundahanar Naira miliyan 64.
Tsofaffin mukarraban sun hada da Lawal Adebisi, tsohon mai bai wa gwamna shawara, Umar Waziri, tsohon Akanta Janar da Yusuf Inuwa, tsohon kwamishinan kudi.

Asali: Twitter
Ana zargin mukarraban El-Rufai da satar N64m
A sanarwar da ICPC ta fitar a shafinta na intanet, kakakin hukumar, Demola Bakare, ya ce za a gurfanar da mutanen tare da wani kamfani mai suna Solar Life Nigeria Limited a kotu

Kara karanta wannan
Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi mutanen da karkatar da kudaden gwamnati zuwa asusun kamfanin Solar Life Nigeria Limited, wanda ake zargin Lawal shi ne mai hannu a kai.
A cikin karar, ICPC ta zargi Lawal da yin aiki tare da sauran wadanda ake tuhuma wajen karkatar da Naira miliyan 64.
An sanya ranar gurfanar da yaran El-Rufai
Kudin da ake zargi sun hada da Naira miliyan 10, miliyan 47.84 da miliyan 7.32, wanda aka ce sun shiga asusun kamfanin.
Kakakin ICPC ya ce za a gurfanar da mutanen a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar 17 ga watan Janairun 2025.
Haka kuma, ICPC ta zargi tsohon shugaban ma’aikata da kwamishinan kudi na El-Rufai, Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu, da yin harkallar N155m.
ICPC ta sake gurfanar da Bashir Sa'idu
Hukumar ta ce Sa’idu ya bayar da kudaden ga Ibrahim Muktar, ma’aikacin ma’aikatar kudi ta jihar Kaduna, ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan
Rigima ta kunno kai a Kudu kan kafa shari'ar Musulunci, an gano inda matsalar take
Wannan zargi ya biyo bayan wata tuhumar almundahana da aka shigar kan Sa'idu a babbar kotun tarayya dake Kaduna makon da ya gabata.
ICPC ta ce an wawure kudaden ne a tsakanin ma’aikatan gwamnatin jihar da masu hannu wajen gudanar da ayyukan kudi.
Majalisar Kaduna na zargin gwamnatin El-Rufai
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ce gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi zambar N423bn, zargin da tsohon gwamnan ya musanta.
El-Rufai ya ce ba shi da hannu a duk wani zargi na cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa na shekaru takwas.
An bukaci jama’a su saurari ci gaba da shari’ar a kotu, yayin da ICPC ta ba da tabbacin yin adalci a kan dukkan zarge-zargen.
Kotu ta hana belin Bashir Sa’idu
A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun jihar Kaduna ta hana belin Bashir Sa'idu. tsohon shugaban ma’aikatan fadar Nasiru El-Rufai, yayin da ake ci gaba da shari’a.
An gurfanar da Sa’idu bisa zargin almundahana, inda kotun ta dage yanke hukunci kan neman belinsa zuwa ranar 16 ga Janairu, 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng