'Yan Sanda Sun Sanya Dokar Hana Fita a Jihar Gombe, Kwamishina Ya Faɗi Dalili

'Yan Sanda Sun Sanya Dokar Hana Fita a Jihar Gombe, Kwamishina Ya Faɗi Dalili

  • Kwamishinan 'yan sandan Gombe, Bello Yahaya, ya ce rundunar ta sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe 12:00 na dare zuwa 5:00 na asuba
  • Yahaya ya bayyana cewa amfani da miyagun kwayoyi yana haddasa karuwar aikata laifuka, musamman a tsakanin matasa a jihar Gombe
  • Da ya karbi bakuncin wata kungiyar fararen hula a Gombe, kwamishinan ya bayyana dalilin 'yan sanda na sanya dokar zaman gida a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Kwamishinan 'yan sandan Gombe, Bello Yahaya, ya bayyana dalilin da yasa rundunar ta kakaba dokar hana zirga-zirga a fadin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar 'yan sandan ta sanya dokar zaman gida a Gombe daga karfe 12:00 na dare zuwa karfe 5:00 na Asubah.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana dalilin sanya dokar hana fita ta awanni biyar a jihar Gombe
Rundunar 'yan sandan Gombe ta sanya dokar hana zirga-zirga daga 12:00 na dare zuwa 5:00 na Asubah. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Dalilin sanya dokar hana zirga-zirga a Gombe

Bello Yahaya ya ce amfani da miyagun kwayoyi yana haddasa karuwar aikata laifuka, musamman a tsakanin matasa da yara ƙanana a jihar, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi abin da ya sa a gaba bayan kammala aikin matatar $20bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya bayyana cewa dokar da aka sanya wata matakin gaggawa ce da aka ɗauka don dakile ayyukan bata-gari a lokacin da mutane ke barci.

Ya kara da cewa karin yawan jami'an tsaro a wuraren taruwar jama’a zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyi daga barazanar 'yan ta’adda.

Bello Yahaya ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin ƙungiyar fararen hula ta Gombe Network da ta kai masa ziyara a shelkwatar rundunar.

A cewarsa:

"Matsalar tsaro mafi girma yanzu ita ce matasa ƙanana da ake koya wa amfani da miyagun kwayoyi da kuma sanya su a ayyukan da ba su dace ba."

Barazanar shan kwayoyi ga matasan Gombe

Tribune ta rahoto kwamishinan ya yi gargadin cewa idan ba a dakile wannan matsala ba, jihar na iya fuskantar barazana mai girma a shekaru masu zuwa.

"Da zarar wadannan yara sun girma cikin shekaru biyar, za su zama manyan masu aikata laifuffuka," in ji Bello Yahaya.

Kara karanta wannan

Natasha: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga, sun harba barkonon tsohuwa

Kwamishinan ya ce tun bayan karɓar aikinsa, matsalar rashin kwanciyar hankali da daddare ta kasance babban ƙalubale da jama’a ke fuskanta.

Kwamishinan ya ce:

"Da rana babu wata barazana, amma dare na yi mutane ke shiga damuwa. Za su yi kasuwanci da rana amma su kasa hutawa da dare saboda 'yan ta'adda."

Yawancin wadanda ake kamawa matasa ne

Kwamishinan 'yan sanda ya fadi tasirin da kwayoyi ke yi kan matasan jihar Gombe
'Yan sanda sun fara cafke matasan Gombe da ke aikata laifuffuka da tsakar dare. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Bello Yahaya ya ce rundunar ta tsara dabarun dakile laifuffuka, inda suka yanke shawarar rufe hanyoyi da dare domin hana zirga-zirga.

Ya jaddada cewa ba wani mutum mai hankali da zai rika yawo da tsakar dare, don haka ya ce, "Ko da kai dan ta'adda ne, je ka kwanta barci."

-Inji kwamishinan.

Kwamishinan ya bayyana cewa wannan matakin ya fara haifar da sakamako mai kyau, inda jama’a ke yaba kokarin 'yan sandan.

Ya ce yawancin mutanen da ake kamawa a kowace rana ana samunsu cikin tasirin miyagun kwayoyi, kuma mafi yawan su matasa ne.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

'Ana shirin aikata laifuffuka a Gombe' - 'Yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Gombe ta ce ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa batagari na shirin aikata laifuffuka a jihar.

Saboda samun wannan rahoto, rundunar ta sanar da sanya dokar takaita zirga-zirga a Gombe daga karfe 12:00 na dare zuwa 5:00 na Asuba domin dakike barazanar tsaron.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.