Rikicin Kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar ta-baci a wasu yankuna 7

Rikicin Kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar ta-baci a wasu yankuna 7

  • Yayin barkewar sabon rikicin kabilanci a jihar Gombe, gwamnati ta sanya dokar hana fita
  • An sanya dokar ne a wasu yankuna bakwai na karamar hukumar Balanga a kudancin jihar
  • Rundunar 'yan sanda tuni ta runtuma zuwa yankin domin kwantar da tarzomar da ta taso

Jihar Gombe - A ranar Talata ne Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kan wasu al’ummu bakwai da ke karamar hukumar Balanga ta jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ismaila Uba-Misilli, Darakta-Janar na harkokin yada labarai, na gidan gwamnatin Gombe ya fitar.

Mista Uba-Misilli ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Njodi ne ya bayyana hakan.

An ruwaito Mista Njodi yana cewa matakin ya biyo bayan sake barkewar rikici tsakanin kabilun Lunguda da Waja a cikin al'ummomin a safiyar Talata 27 ga watan Yuli, VON ta ruwaito.

Rikicin Kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar ta baci a wasu yankuna 7
Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Sanarwar ta zayyana al'ummomin da abin ya shafa da suka hada da Nyuwar, Jessu, Heme, Yolde Gelentuku, Sikam, Wala-Lunguda da kewayenta, inda ta kara da cewa dokar hana fitan ta fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Matafiya tara aka sace a hanyar Sokoto-Gusau ba 60 ba – ‘Yan sanda

An ruwaito Njodi yana fadar haka a cikin sanarwar:

“Dokar hana fita ta zama wajibi don maido da doka da oda a yankunan da abin ya shafa.
“An tura jami’an tsaro don farfado da al’amuran yau da kullun yayin da dokar hana fita za ta ci gaba har zuwa wani lokaci.”

Meye kwamishinan 'yan sandan jihar ya fada dangane da rikicin?

A halin da ake ciki, Ishola Babaita, kwamishinan ‘yan sanda a jihar, ya tabbatar da tashin hankalin da ya barke a Balanga, yana mai cewa isassun 'yan sanda da sauran jami’an tsaro sun dira zuwa yankunan da abin ya shafa, in ji Daily Nigerian.

“Ba mu bar wurin ba dama, amma yanzu mun kara karfafa jami'ai a wurin yanzu.

Ya kuma bayyana cewa, jami'an na aiki don sanya ido kan dukkan zirga-zirga a yankunan, ya kuma gargadi mutane game da daukar doka a hannunsu.

Kwamishinan ya ce:

"Babu wani korafi da zai bayar da damar daukar makami a kan kowa."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Sojoji sun garkame kasuwannin jihar kudu saboda nuna goyo baya ga Nnamdi Kanu

A wani labarin, Jihar Imo - Sojoji a ranar Talata sun hana ‘yan kasuwa a kasuwannin katako da na kayayyakin gini a Orlu, jihar Imo, budewa domin gudanar da kasuwancinsu na ranar.

Mafi yawan ‘yan kasuwar a kasuwannin biyu a ranar Litinin din da ta gabata sun ki bude shagunansu don nuna goyon baya ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar tuhumar ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Sojojin, wadanda ke gudanar da aikin shingen binciken ababen hawa kusa da manyan kasuwannin biyu a Orlu, sun hana ‘yan kasuwar bude shagunansu da duk wata harkar kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.