Ramadan: An Fadi Dalilin Faduwar Farashin Abinci Karon Farko cikin Shekaru 10 a Azumi
- Tsohon mai ba da shawara na shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya yabi shugaba Bola Tinubu saboda raguwar farashin abinci a lokacin azumin Ramadan
- Omokri ya kira wannan ci gaba da suna "Tasirin Tinubu," yana mai cewa wannan ne karo na farko a cikin shekaru 10 da farashin abinci ya ragu
- Ya ce, a baya, farashin kayan abinci yana ƙaruwa a Ramadan, amma a bana, duk da cewa azumin Lent na Kiristoci sun zo tare, hakan bai faru ba
- Ya jaddada cewa kokarin Gwamnatin Tarayya, musamman ta ofishin Nuhu Ribadu, ya taimaka wajen kare amfanin gona fita ƙasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon mai ba da shawara na shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya kwarara yabo ga Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Omokri ya yabi Tinubu ne saboda abin da ya kira babban ci gaba a karo na farko da farashin abinci ya ragu a lokacin Ramadan.

Asali: Facebook
Omokri ya yabawa salon mulkin Tinubu
Omokri ya bayyana haka a jiya Laraba 5 ga watan Maris, 2025 a shafinsa na X inda ya ce duka kokarin Tinubu ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hadimin na Mai girma Goodluck Jonathan ya bayyana wannan ci gaba a matsayin "Tasirin Tinubu,"
A rubutunsa, yana mai cewa raguwar farashin abinci ya saba da yadda a baya kudin ya ke ƙaruwa a kasuwa yayin Ramadan.
Ya ce:
"Duk shekara a cikin shekaru 10 da suka gabata, farashin abinci yana ƙaruwa a farkon Ramadan, 2025 ne karo na farko da farashin abinci ya ragu."
"Kuma abin ban mamaki shi ne a bana, Ramadan da azumin Lent na Kirista sun zo a lokaci guda. Wannan ya kamata ya haifar da hauhawar farashin abinci.
"Amma abin da muke gani akasin haka ne, me ya sa? Wannan shi ne Tasirin Tinubu, sakamakon kyakkyawan shugabancin da Ofishin Nuhu Ribadu ke yi wajen kula da tsaron abinci a Najeriya."

Asali: Twitter
'Akwai tasirin Nuhu Ribadu' - Reno Omokri
Omokri ya kuma jaddada cewa, ofishin Nuhu Ribadu ba wai kawai yana kula da tsaron ƙasa ba ne, har da tsaron abinci, man fetur da wutar lantarki.
Ya ce Ribadu ba wai yana maida hankali kan tsaron lafiyar jiki kadai ba, a sakamakon haka, ƙididdigar ta'addanci ta Najeriya ta inganta daga 8.065 a 2023 zuwa 7.577.
Ya kara da cewa:
"Ribadu yana kuma maida hankali kan tsaron abinci da sauran bangarorin tsaro, kamar tsaron man fetur da wutar lantarki.
"A kokarinsa, Ribadu ya dakatar da fitar da kayayyakin abinci daga Najeriya zuwa ƙasashe makwabta a lokutan bukukuwa, tare da samar da tsaro ga manoma da matsalolin tsaro suka hana su yin noma a baya."
Hutun Ramadan: Omokri ya gargadi kungiyar CAN
Kun ji cewa tsohon hadimin shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya saba da kungiyar Kiristoci ta CAN game da yi wa jihohin Arewa barazana saboda hutun makarantu.
Omokri ya ce babu dalilin tayar da hankali kan batun, duba da yadda Musulmi ke hakuri da hutun da ke fifita Kiristoci a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng