Yadda Farashin Abinci Ke Faduwa Ana Azumin Ramadan, Masana Sun Yi Hasashe

Yadda Farashin Abinci Ke Faduwa Ana Azumin Ramadan, Masana Sun Yi Hasashe

  • Yayin da aka fara azumi, Farashin hatsi kamar su shinkafa, masara da gero yana sauka a wasu jihohin Arewacin Najeriya
  • Masana sun danganta hakan da karancin kudi kuma akwai zargin yawan shigo da kayayyaki da ake yi a yan kwanakin nan
  • A Kaduna da Taraba, farashin wake, shinkafa da masara ya ragu inda buhun masara a Taraba ya koma N45,000 daga N57,000
  • A jihohin Kano da Niger, farashin kayan abinci kamar wake da gero sun ragu sosai a lokacin da aka san abinci da yin tsada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Yayin da aka fara azumin watan Ramadan, farashin kayayyakin abinci kamar masara, shinkafa, gero da wake ya ragu a wasu jihohin Arewa.

Wasu masana sun yi hasashen haka tun kwanaki da suka gabata da suke ganin hakan na da alaƙa da yawan kayan abinci da ake shigo da shi.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, NNPCL ya yi maganar saukar farashin fetur da kara gidajen mai

Yadda ake ci gaba da samun raguwar farashin kayan abinci
Masana sun yi hasashen musabbabin faduwar farashin kayan abinci. Hoto: Hassan Ahmad.
Asali: Facebook

Masana sun yi hasashen dalilin faduwar farashi

Binciken Aminiya ya nuna cewa raguwar farashin ya fi yawa a jihohin da ake noma mafi yawan wadannan kayayyaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na faruwa ne bayan daukar azumin farko na watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar 1 ga watan Maris, 2025.

Masana sun bayyana cewa faduwar farashin na da nasaba da karancin kudi a hannun jama’a, da yadda bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara suka shafi kasuwa.

Wasu kuma sun danganta hakan da yawan shigo da kayan amfanin gona a baya-bayan nan.

A kasuwanni daban-daban, an samu saukin farashi, misali, buhun fulawa mai nauyin kilo 50 da aka sayar da shi kan N80,000 yanzu yana tsakanin N61,000 zuwa N63,000.

A kasuwar Saminaka ta Kaduna, buhun masara mai kilo 100 da ake sayarwa N70,000 zuwa N75,000 yanzu ya koma N47,000, haka kuma waken soya daga N110,000 ya koma N68,000.

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur

Ana samun karyewar farashin abinci a Arewacin Najeriya
An samu faduwar farashin hatsi a kasuwannin Neja, 'yan kasuwa da manoma sun koka. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Yadda farashin ya ke a Taraba da Kano

A kasuwar Mutum Biyu ta Taraba, farashin buhun shinkafa mai kilo 100 da ya kai N50,000 a watan da ya gabata, yanzu ya ragu zuwa N45,000.

Haka kuma buhun masara daga N57,000 ya koma tsakanin N40,000 zuwa N45,000.

A Kano, kwanon wake a kasuwar Danhassan ya ragu daga N3,500 zuwa N2,500, yayin da kwanon masara a Kasuwar Dawanau ke tsakanin N1,200 zuwa N1,300.

A jihar Niger, buhun jan wake ya fadi daga N200,000 zuwa N90,000, farin wake daga N160,000 zuwa N90,000, yayin da buhun masara daga N85,000 ya koma N40,000.

A kasuwar Gombe, farashin buhun shinkafa mai kilo 100 da ya kai N180,000 ya ragu.

Wannan raguwar farashi abin farin ciki ne ga masu siya, sai dai wasu manoma na nuna damuwa game da faduwa da suke yi.

An kaddamar da bikin karya farashin abinci

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fitar da sanarwa kan ganin watan Ramadan na 2025

Kun ji cewa wasu yan kasuwa sun yi bikin karya farashin kayan abinci a jihar Kano ana shirin fara azumin watan Ramadan.

Wannan na zuwa ne bayan halin da aka shiga a baya na tsadar kayan abinci wanda a yanzu a ke samun sauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.