Kano Sabuwa: Abba Zai Sake Tura 'Ya 'Yan Talakawa Sama da 1000 Karatu Kasar Waje
- Gwamnatin Kano ta bayyana shirin daukar nauyin dalibai 1,002 don tura su karatu kasashen waje, kari kan 1,001 da aka tura a 2024
- Mataimakin gwamna, Aminu Gwarzo ya ce shirin zai bai wa matasan Kano damar samun ingantaccen ilimi, tare da gina basirar su a duniya
- Kwamared Gwarzo ya yi maganar yayin wata ziyarar girmamawa da tawagar Tarayyar Turai (EU) ta kai masa gabanin baje kolinsu a Kano
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf ta bayyana shirin daukar nauyin dalibai 1,002 domin karatu a kasashen waje.
Wannan zai zama ci gaba daga nasarar da gwamnatin jihar ta samu a shekarar da ta gabata, inda aka tura dalibai 1,001 karatu kasashe daban-daban.

Asali: Twitter
Mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya bayyana hakan, kamar yadda hadimin gwamnan, Abdullahi I. Ibrahim ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano za ta tura dalibai karatu waje
Sanarwar Abdullahi ta ce Kwamared Aminu ya yi maganar ne yayin wata ziyarar girmamawa da tawagar Tarayyar Turai (EU) ta kai masa.
An ce tawagar Turan ta ziyarci mataimakin gwamnan ne gab da bikin baje kolin damammakin karatu a Turai da za a gudanar a Kano, a 2025.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar, Gwarzo ya bayyana shirin a matsayin wani mataki mai muhimmanci da zai bai wa matasan Kano ilimi.
Kwamared Gwarzo ya ce tura yara su yi karatu a kasashen ketare zai ba su damar goga kafada a harkar ci gaban atattalin arziki na duniya.
Kano ta ware manyan kudi domin ilimi
Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa jihar Kano ta fi kowace jiha a Najeriya ware kasafin kudi mai yawa don bangaren ilimi a shekarun 2024 da 2025.
"Mun ayyana dokar ta-baci kan ilimi don tabbatar da cewa matasanmu sun samu ingantaccen ilimi," inji Kwamared Gwarzo.
Ya kuma yaba da hadin gwiwar jihar da Tarayyar Turai, yana mai cewa bikin baje kolin karatu a Turai zai samar da damarmakin karatu ga dalibai da malaman Kano.
Gwarzo ya bayyana Kano a matsayin jiha mai dogon tarihi a fannin kasuwanci, al’adu, da ilimi, yana mai cewa hadin gwiwa irin wannan zai bunkasa cigaban jihar da Najeriya baki daya.
"Muna sa ran wani taro mai alfanu da zai kara karfafa matasanmu, inganta musayar ilimi, da taimakawa ci gaban Kano, Najeriya, da yankin yammacin Afirka.'
- Kwamared Gwarzo.
Jakadan EU ya fadi muhimmancin hadin gwiwa

Asali: Twitter
Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS, Gautier Mignot, ya bayyana cewa bikin baje kolin ilimi a Turai da za a gudanar a ranar 27 ga Fabrairu, 2025, zai karfafa musayar ilimi da hadin gwiwa tsakanin jami’o’in Turai da daliban Kano.
Ya ce bikin na baya ya bai wa dalibai damar haduwa kai tsaye da wakilan jami’o’in Turai, inda aka kulla sababbin yarjejeniyoyin karatu da musayar ilimi.
"Muna fatan kafa sababbin hadin gwiwar ilimi, wanda zai bai wa daliban Kano damar yin karatu a Turai, yayin da malamai daga Turai za su iya zuwa Kano don koyarwa,"
- inji Mignot.
Ya bayyana cewa jami’o’i 20 daga kasashe daban-daban na EU za su halarci taron, kuma da yawansu wannan ne karon farko na zuwansu Kano.
Wakilan EU da suka halarci taron
Tawagar Tarayyar Turai da ta halarci taron sun hada da:
1. Ambasada Michal Cygan – Jakadan Poland a Najeriya
2. Jurgew Bartelink – Mataimakin jakada, ofishin jakadancin Netherlands a Najeriya
3. Leila Ben Mathieu – Shugabar sashen cigaban dan Adam, EU a Najeriya
4. Kristof Korosi – Mataimakin jakadan Hungary a Najeriya
Gwamnatin Kano ta ce wannan shiri zai taimaka wajen cika muradin gwamnatin Abba na bunkasa ci gaban matasa, ta hanyar samar musu da damar samun ilimi a matakin duniya.

Kara karanta wannan
Soyayya ta ƙare: Wani ɗan Najeriya ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta mutu
Abba ya ziyarci daliban Kano a India
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa ɗaliban da gwamnatinsa ta tura Indiya, yana mai yaba ƙoƙarinsu da nasarorin da suka samu.
Ya ce ziyararsa ta ba su damar bayyana ƙalubale, tare da tabbatar da cigaba da tallafin karatu har ƙarshen wa’adinsa na farko.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng