Kasashe 6 da zaku iya yin karatun digiri da digirgir kyauta a Turai

Kasashe 6 da zaku iya yin karatun digiri da digirgir kyauta a Turai

-Tsadar kudin makaranta na hana matasa da sama yin karatu

-Ilimi yana da matukar muhimmanci a rayuwa

-Akwai kasashen dake bayar da ilimi kyauta

Tsadar kudin makaranta na daga cikin manyan matsaloli dake hana wasu daga cikin jama’a samun damar yin karatun jami’a, kuma matsalar na addabar mutanen kasashe da dama, daga ciki harda kasashen da suka cigaba, irin su Amurka da Ingila.

Amma duk da wannan matsala ta tsadar kudin makaranta, akwai kasashen da ake yin karatun jami’a cikin harshen turanci kyauta. Wadannan kasashe su ne;

1. Norway

Kasar Norway nada tsananin sanyi sannan ga tsadar rayuwa duk da kasancewar jami’o’in gwamnatin kasar kyauta suke bayar da ililimi ga dalibai, na gida dana waje. Akwai manyan jami’o’I da suka yi shura a duniya a kasar Norway da suka hada da; jami’ar birnin Oslo, Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta kasar Norway, da kuma jami’ar Bergen.

Kasashe 6 da zaku iya yin karatun digiri da digirgir kyauta a Turai
Kasashe 6 da zaku iya yin karatun digiri da digirgir kyauta a Turai

2. Finland

Kafin shekarar 2017, karatu a jami’o’in kasar Finland kyauta ne. Saidai a halin yanzu, duk mai bukatar yin karatun jami’a a kasar, sai ya biya mafi karancin kudin makaranta Dala 1,650 a shekara, adadin kudin ya banbanta bias abinda mutum zai karanta. Dalibai masu burin yin digiri na biyu dana uku a kasar Finland, ba sai sun biya ko sisi ba domin gwamnatin kasar ta daukewa daliban kasashen ketare biyan kudin makaranta.

DUBA WANNAN: Babban Bankin kasa zai haramtawa masu taurin bashi samun rance daga Bankuna

3. Sweden

Karatun digiri na uku a kasar Sweden kyauta ne, amma fa a bangaren da ya shafi binciken kimiyya. Akwai tsananin tsadar rayuwa a kasar Sweden.

4. Jamus

Karatun jami’a a kasar Jamus kyauta ne ga daliban kasashen ketare, saidai akwai bukatar mutum ya mallaki gogewar aiki kafin samun gurbin karatu a jami’o’in kasar. Jami’o’in kasar Jamus na daga cikin jami’o’i masu daraja a duniya.

5. Slovenia

Jami’o’in kasar Slovenia na yin karatu ne cikin harshen turanci, sannan kasar nada kusanci da kasashen Italiya da Kuroshiya; kasashen da jama’a ke kaunar zuwa yawon bude ido. Ga masu son samun saukin karatu, kasar Slovenia na yi maku maraba domin kuwa jami’o’in kasar kyauta suke bayar da ilimi kuma cikin harshen ingilishi.

6. Faransa

Kasar Faransa ta canja tsari, yanzu zaku iya yin karatu a kasar ba tare da kuna jin faransanci ba. Kudin da ake biya a jami’o’in kasar Faransa basu taka kara sun karya ba, sannan ana la’akari da karfin tattalin arzikin mutum wajen yanke masa adadin kudin makaranta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng