Gwamna Kirista Ya Bukaci Dukan Ciyamomi a Jiharsa Su Dauki Nauyin Mahajjaci 1
- Gwamnatin jihar Ebonyi ta bukaci shugabannin kananan hukumomi 13 su dauki nauyin akalla Mahajjaci daya don aikin Hajjin 2025
- Majalisar zartarwa ta jihar ta amince da kashe N500m domin daukar nauyin Mahajjata 46, yayin da kowane shugaban karamar hukuma zai dauki guda daya
- Wasu mazauna jihar sun yi tir da matakin, suna mai cewa ana da sauran matsaloli kamar yajin aikin malaman firamare da ya kamata a warware
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Abakaliki, Ebonyi - An yi ta ce-ce-ku-ce bayan Gwamnatin jihar Ebonyi ta bukaci shugabannin kananan hukumomi 13 da su dauki nauyin akalla Mahajjaci daya a 2025.
Gwamnatin Francis Nwifuru ta bukaci hakan daga shugabannin kananan hukumomi don aikin Hajjin shekarar 2025 a Saudiyya.

Asali: Twitter
Gwamna Kirista ya dauki nauyin Musulmai zuwa hajji
Leadership ta ce bayan taron majalisar zartarwa, gwamnati ta bayyana cewa an amince da N500m don daukar nauyin Mahajjata 46 domin aikin Hajjin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a, Mista Jude Okpor, ya ce gwamna ya bukaci shugabannin kananan hukumomi su dauki nauyin akalla musulmi daya daga kowace karamar hukuma zuwa aikin Hajji.
Mista Okpor ya ce:
“Najeriya kasa ce mai bin tsarin addini daban-daban, kuma jihar Ebonyi kasa ce da ke cike da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai."
“A matsayin wani mataki na nuna kyakkyawan shirin wannan gwamnati, majalisar zartarwa ta amince da sakin N551,502,142.84 domin daukar nauyin Mahajjata 46 don aikin Hajjin 2025.”
"Adadin kudin da aka ware yana nufin cewa kowane Mahajjaci zai samu N8,784,085.59 a wannan shirin."
"Majalisar ta kuma yanke shawarar cewa shugabannin kananan hukumomi su dauki nauyin mutum daya daga kowace karamar hukuma don aikin Hajjin 2025 domin fadada damar shiga ga 'yan asalin jihar."
Mazauna Ebonyi sun caccaki Gwamna Nwifuru
Sai dai wasu mazauna jihar sun nuna damuwa game da wannan mataki na gwamnati yayin da malaman makarantar firamare ke yajin aiki saboda rashin biyansu albashi.
Wani tsohon malami kuma mai ritaya, Mista Clifford Agwu, ya ce:
“Shin menene fifiko? Aiki Hajji ko biyan malaman makaranta albashi? Shugabannin kananan hukumomi sun ki biyan malamai, kuma suna yajin aiki amma gwamna ba zai tilasta su ba.”
"Me yasa gwamnati za ta bukaci shugabannin kananan hukumomi su kashe kusan miliyan 10 kowanne wajen daukar nauyin Mahajjata, alhali malaman makaranta suna gida saboda ba a biya su albashin wata uku ba?"
Legit Hausa ta tattauna da dan jihar Ebonyi
Joshu'a Chukwudi ya ce hakan ba matsala ba ne amma bangaren ciyamomin ne damuwa saboda matsaloli da ke tattare da su.
Ya ce saboda hakan bai wuce kara kawo hadin kai ba ne tsakanin mabambantan addinai a jihar da aka santa da zaman lafiya.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya na fuskantar barazana daga Trump, Amurka ta dakatar da ayyukan USAID
"Daman an saba yi duk shekara ana daukar nauyin wasu amma ciyamomi suna matsaloli a yankunansu da ya kamata su magance."
- Cewar Joshu'a
Matashin ya bukaci gwamnatin jihar ta kawo dauki musamman a yankunan karkara da ke fama da matsalolin tsaro.
Gwamnan APC ya halarci taron jam'iyyar LP
A baya, kun ji cewa Gwamnan jihar Ebonyi ya jagoranci kusoshin APC sun halarci taron rabon tallafi na ɗan majalisar tarayya na jam'iyyar LP.
Gwamna Francis Nwifuru ya bayyana cewa ya halarci taron ne saboda siyasa ba gaba ba ce kuma ɗan majalisar abokinsa ne.
Asali: Legit.ng