Rabo Dangin Ajali: Gwamna Ya Dawo da Kwamishinoni 3 da Ya Dakatar, Ya Nada Mukamai
- Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya dawo da kwamishinonin da aka dakatar, ciki har da na Kananan Hukumomi, Lafiya, da Albarkatun Ruwa
- An dakatar da su ne bayan da aka gano an karkatar da kayayyakin gwamnati inda Gwamnan ya bayar da umarnin kama wasu mutane shida
- A yayin wani bauta a coci, gwamnan ya sanar da sabbin shugabannin Jami’ar Ebonyi da kuma nada sabon shugaban hukumar gyaran titunan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Abakaliki, Ebonyi - A ƙarshe, Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya dawo da kwamishinonin uku da ya dakatar.
Kwamishinonin sun hada da na Kananan Hukumomi, Mista Uchenna Igwe, da na Ma’aikatar Lafiya, Dakta Moses Ekuma, da na Albarkatun Ruwa, Mista Chinedu Nkah.

Asali: Twitter
Gwamna ya dakatar da kwamishinoni a jiharsa
Gwamnan ya kuma dawo da Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya, Dakta Lawrence Ezeogo, da Sakatare na Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Ebonyi, Dakta Emeka Ovuoba, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya, gwamnan ya dakatar da wadannan manyan jami’an gwamnati bayan da ya gano an karkatar da wasu kayayyakin gwamnati.
Daga nan sai ya bayar da umarnin kama da gurfanar da Mista Ndukwe Ayansi da wasu mutane biyar da ake zargi da karkatar da kayayyakin Ma’aikatar Lafiya.
Gwamnan ya gano wata motar Toyota da ke dauke da rijistar marasa lafiya, littattafai, da wasu kayayyaki daga sito na ma’aikatar ba tare da izini ba.
Haka nan, an dakatar da kwamishinonin Albarkatun Ruwa da Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta saboda wasu zarge-zargen da ba su dace da aikinsu ba.
Gwamna ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa
Gwamna Nwifuru ya bayyana hakan ne yayin wani bauta a cocin Sabon Gidan Gwamnati da ke Centenary City a Abakaliki, babban birnin jihar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu
A yayin ibadar coci, gwamnan ya sanar da sabbin shugabannin Jami’ar Ebonyi bayan karewar wa’adin tsohon shugaban jami’ar, Farfesa Chigozie Ogbu.
Gwamnan ya nada Farfesa Michael Awoke Ugota a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar, tare da wasu sabbin mukamai a jami’ar.
Haka nan, ya nada Mista Ben Nwovu a matsayin sabon shugaban Hukumar Gyaran Tituna ta Jihar Ebonyi.
Gwamna Kirista ya dauki nauyin mahajjata
A baya, kun ji cewa Gwamnatin jihar Ebonyi ta bukaci shugabannin kananan hukumomi 13 su dauki nauyin akalla Mahajjaci daya don aikin Hajjin 2025.
Majalisar zartarwa ta jihar ta amince da kashe N500m domin daukar nauyin Mahajjata 46, yayin da kowane shugaban karamar hukuma zai dauki guda daya.
Asali: Legit.ng