An Gano Wadanda Suka Taimaka Aka Sace Tsohon Shugaban NYSC a Katsina

An Gano Wadanda Suka Taimaka Aka Sace Tsohon Shugaban NYSC a Katsina

  • Shugaban karamar hukumar Bakori, Hon. Ali Mamman Mai Chita, ya yi bayani a kan sace tsohon babban jami'in rundunar sojin kasar
  • Ya tabbatar da cewa masu ba da bayanai ga ‘yan bindiga ne suka taimaka wajen sace tsohon Janar din a gidansa ba tare da sun samu cikas ba
  • 'Yan bindigan da su ka yi garkuwa da Manjo-Janar Maharazu Tsiga sun tuntubi iyalansa, suka bukaci a biya su N250m kafin su sako shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Shugaban karamar hukumar Bakori a jihar Katsina, Hon. Ali Mamman Mai Chita, ya bayyana cewa masu ba ‘yan bindiga bayanan sirri ne suka haddasa sace tsohon Darakta Janar na NYSC, Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya).

Kara karanta wannan

'Dan Majalisa ya fito ya faɗi gaskiya, ya bayyana kuɗin da aka tura wa ƴan bindiga

An yi garkuwa da Manjo-Janar Maharazu mai ritaya tare da wasu mutum tara a yankin Tsiga na karamar hukumar Bakori.

Tsiga
An dora alhakin sace babban jami'in rundunar soja a kan 'infoma' Hoto: Abdullahi Tsiga
Asali: Facebook

Thisday ta wallafa cewa 'yan bindigar sun tuntubi 'yan uwan tsohon shugaban NYSC, inda suka bukaci a biya su kudin fansa na Naira miliyan 250 kafin su sake shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga suka sace Janar Tsiga

Da yake magana da manema labarai a Bakori a ranar Litinin, Hon. Mai Chita ya ce ba tare da taimakon masu ba da bayanai ba, babu yadda za a yi a sace tsohon Janar na soji a gidansa.

Ya ce:

“Idan ba don masu ba da bayanai ba (infoma), wa zai iya zuwa gidan tsohon Janar na soji ya sace shi? Wannan aikin masu ba da bayanai ne. Allah Ya shiga tsakaninmu da su."

Katsina: Ana kokarin ceto tsohon shugaban NYSC

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda, sojoji, ‘yan sandan sa-kai na Katsina Community Watch Corps da ‘yan banga, na cigaba da kokari don ceto Tsiga da sauran wadanda aka sace ba tare da sun samu rauni ba.

Kara karanta wannan

Harsashi ya kare wa dan bindiga yana musayar wuta da sojojin Najeriya

Ya kara da cewa dabarun tsaro da gwamnatin jihar Katsina ke amfani da su sun taimaka wajen rage matsalolin tsaro a Bakori da sauran kananan hukumomi makwabta.

Ya ce:

“An samu ingantacciyar tsaro a karamar hukumar Bakori da 80% saboda kokarin Gwamna Dikko Umaru Radda da jami’an tsaro.”

Shugaban karamar hukumar ya dora alhakin matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan jihar a kan masu ba da bayanai ga ‘yan bindiga da hadin gwiwar masu taimaka musu.

An sace tsohon janar a kauyen Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun afka garin Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina, suka sace Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya).

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar da yawansu ya kai 100 sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12:30 na tsakar dare a ranar Alhamis, inda suka kutsa yankin ba tare da wata fargaba ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindigan da suka sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga sun turo saƙo a Katsina

Sace Janar Tsiga da sauran mutanen yankin ya jefa mazauna Tsiga cikin tsananin fargaba da tashin hankali, yayin da wasu daga cikin wadanda suka shaida harin sun ce an yi gaggawar sanar da hukumomin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.