'Dan Majalisa Ya Fito Ya Faɗi Gaskiya, Ya Bayyana Kuɗin da Aka Tura Wa Yan Bindiga
- Ɗan Majalisa a jihar Edo ya musanta ikirarin ƴan sanda da rundunar tsaron gwamna game da batun ceto Mai Martaba Friday Ehizojie
- Hon. Inegbeboh Ojie Eugene ya ce ikirarin da jami'an tsaro suka yi cewa su suka ceto basaraken ba gaskiya ba ne, sai da aka biya kuɗin fansa
- Ya ce al'ummar masarautar Udo-Eguare ne suka yi karo-karo suka haɗa kudin fansar suka biya ƴan bindiga kafin sako sarkinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Igueben a Majalisar Dokokin Jihar Edo, Hon. Inegbeboh Ojie Eugene, ya yi karin haske kan yadda aka ceto sarkin Udo-Eguare.
Ɗan Majalisar ya bayyana cewa al’ummar Udo-Eguare sun biya kudin fansa kafin ‘yan bindiga su sako sarkinsu, Mai Martaba Friday Ehizojie.

Asali: Original
Daily Trust ta tattaro cewa an sace basaraken ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025 da yake tafiya a kan babur, kuma ƴan bindigar sun sako shi bayan kwana uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nawa aka turawa ƴan bindiga kuɗin fansa?
Hon. Eugene, wanda bai bayyana adadin kudin da aka biya ba, ya yi wannan bayani ne a zaman majalisa na ranar Litinin.
Ya bukaci ‘yan sanda da rundunar tsaro ta jihar Edo (ESSC) su daina ikirarin ceto basaraken, domin a cewarsa, ba su da masaniya kan yadda aka sake shi.
A baya dai, rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta sanar da cewa jami’anta tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarauta ne suka ceto basaraken.
Bayan kwanaki biyu, kwamandan ESSC, Mr. Friday Ibadin, shi ma ya bayyana cewa jami’ansa ne suka kubutar da mai martaba sarkin.
Yadda jami'an tsaro suka gaza ceto sarkin
Da yake jawabi a zauren Majalisa a Benin, Hon. Eugene ya ce:
“Mai girma kakakin Majalisa, abin takaici ne a lokacin da lamarin ya faru, na sanar da hukumomin tsaro game da sace sarkinmu domin su dauki matakin da ya dace, amma sai suka nuna kamar suna aiki kuma ba abin da suke yi.
“Ta yaya za su ce sun ceto mutum daga hannun ‘yan bindiga ba tare da an kama ko daya daga cikinsu ba? Shin, zuwa suka yi suka ɗauko sarkin suka dawo da shi gida kurum? Idan har sun san ‘yan bindigar, su nuna mana su.
"Mai girma kakaki, Allah ne kawai ya taimaki al’ummarmu suka tara kudin fansa suka biya aka sako sarkinmu. Don haka, ba wanda zai fito ya yi ikirarin ceto shi, ba gaskiya ba ne."
Ɗan Majalisa ya yabawa gwamnan Edo
'Dan siyasar ya bukaci Majalisar dokokin Edo da ta gayyaci kwamandan ESSC, Mr. Friday Ibadin, domin ya yi bayani kan matakan da hukumar ke dauka don shawo kan matsalar tsaro.
Haka kuma, ɗan Majalisar ya gode wa Gwamna Monday Okpebholo bisa daukar mataki da kuma tallafin da ya bai wa jami’an tsaro a lokacin da lamarin ya faru.
Masu garkuwa da Janar Tsiga sun kira

Kara karanta wannan
Yan sanda sun yi bajinta, sun ceto fitaccen basarake bayan shafe kwanaki a wurin miyagu
Kun ji cewa masu garkuwa da tsohon Darakta Janar na hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 250.
Wani ɗan garin Tsiga ya tabbatar mana da cewa maharan sun tuntubi iyalin dattijon kuma an fara tattaunawa yayin da jami'an tsaro su ke na su ƙoƙarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng