Karshen Alewa: Sojoji Sun Gano Maboyar Bello Turji a Zamfara, Sun Kaddamar da Hari

Karshen Alewa: Sojoji Sun Gano Maboyar Bello Turji a Zamfara, Sun Kaddamar da Hari

  • Sojojin Operation Fansan Yamma sun samu gagarumar nasara yayin da suka farmaki babbar maboyar Bello Turji a Zamfara
  • A yayin farmakin, sojojin sun gano makamai da harsasai, kuma sun rusa sansanin da Turji ke amfani da shi wajen shirya hare-hare
  • Wannan nasara ta kawo cikas ga ayyukan Bello Turji, yayin da sojojin suka kubutar da wasu mata da kananan yara da aka tsare

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Sojojin Operation Fansan Yamma sun samu nasarar tarwatsa maboyar fitaccen ɗan ta’adda, Bello Turji, a jihar Zamfara.

Wannan farmakin ya taimaka wajen gano manyan makamai, abin da ya zama matakin ci gaba a yaki da miyagun laifuffuka a yankin.

Sojojin Najeriya sun farmaki babbar maboyar Bello Turji da ke jihar Zamfara
Sojoji sun kubutar da mata da yara, sun kwato makamai yayin da suka farmaki sansanin Bello Turji. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Dakarun sojoji sun farmaki maboyar Bello Turji

Sojojin Fansan Yamma da ke karkashin Operation Tsatsa Daji III sun ƙara himma wajen kawar da sansanonin ‘yan ta’adda a Shinkafi da Zurmi, inji rahoton Zagazola.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan sirri sun tabbatar da cewa sojojin sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri kan ‘yan ta’adda da suka sake taruwa a kauyen Katsira.

Sojojin ba su gano komai a binciken farko da suka gudanar ba, lamarin da ya sa suka kutsa cikin kauyen Fakai, sananniyar maboyar ‘yan ta’adda.

Sojoji sun tarwatsa Fakai, sun ceto mutane

Sojojin sun tarwatsa Garin Fakai, wacce ta kasance maboyar Bello Turji, ɗaya daga cikin fitattun manyan ‘yan ta’adda a Najeriya.

Majiyoyin soja sun tabbatar da cewa an kona gine-ginen sansanin, yayin da ‘yan ta’adda suka tsere, suka bar mata da yara da ke tsare a hannunsu, waɗanda sojojin suka kubutar.

An rahoto cewa a yayin farmakin, sojojin sun gano bindigogi kirar AK47, bama-baman RPG da harsasai da dama.

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar soji, karkashin Operation Hadarin Daji, ta kara kaimi wajen farautar shugaban 'yan ta’adda, Bello Turji.

Kara karanta wannan

'Ku tuba kafin Ramadan': Dan ta'adda ya gargadi al'umma, ya fadi matakin da zai ɗauka

Wannan bayanin ya biyo bayan rade-radin da ake yi na cewa an cafke Bello Turji, lamarin da rundunar sojojin ta musanta a fili.

Sai dai rundunar sojin ta jaddada cewa ba za ta yi sako-sako ba, har sai an damƙe fitaccen ɗan ta’addan da ya addabi al’umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.