Gwamnan Zamfara Ya Fadi Nasarorin da Aka Samu kan 'Yan Bindiga a Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Fadi Nasarorin da Aka Samu kan 'Yan Bindiga a Jihar

  • Gwamnan jihar Zamfara ya taɓo batun matsalar rashin tsaro da ƴan bindiga wadanda suka addabi jihar
  • Dauda Lawal ya bayyana cewa ana samun tarin nasarori a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga a jihar Zamfara mai arziƙin albarkatun ƙasa
  • Gwamnan ya ba da tabbacin cewa hare-haren ƴan bindiga sun ragu a jihar, kuma ana ɗaukar matakai domin shawo kan matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan matsalar ƴan bindiga da ta addabi jihar.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa na samun ci gaba wajen yaƙi da ƴan bindiga a jihar.

Dauda Lawal ya magantu kan rashin tsaro
Gwamna Dauda Lawal ya ce ana samun nasarori kan 'yan bindiga Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Zamfara ya ziyarci ofishin bankin duniya

Kara karanta wannan

Dan El Rufai ya fadi matsayarsa kan bincikar mahaifinsa ya ba da shawara

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai ofishin babban bankin duniya a Abuja, inda ya gana da daraktan bankin a Najeriya, Dr. Ndiamé Diop.

Tattaunawar ta su ta mayar da hankali ne kan ayyukan ci gaba a fannin ilimi, kiwon lafiya, da noman zamani.

Haka kuma, ana sa ran wannan ziyara za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da bankin duniya.

Me Gwamna Dauda ya ce kan matsalar ƴan bindiga

"Hare-haren ƴan bindiga a hanyoyinmu, ƙauyuka da birane sun ragu sosai. Muna samun ci gaba a yaƙin da muke yi da miyagun laifuka, kuma rayuwa na komawa dai-dai a yankunanmu."
"Hakan yana bayyana ne ta yadda rahotannin hare-haren da ake samu kullum ke ƙara raguwa, da kuma yadda ake aiwatar da ayyukan ci gaba a ko’ina cikin jihar Zamfara."
"Mun fahimci ƙalubalen tsaro da suka shafi aiwatar da ayyukan ci gaba a baya, musamman waɗanda suka hana cimma manufofi saboda matsalolin tsaro da suka hana gudanar da ayyuka yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Zamfara

"Sai dai muna samun ci gaba domin an soma magance matsalar, kuma abubuwa na dawowa daidai."
"Mun ɗauki matakai na ƙarfafa tsaro ta hanyar sa ido sosai, ƙara sintiri da kuma shirin rage barazanar hare-hare."
"Gwamnatina ta ƙudiri aniyar kare rayuka da dukiyoyin al’umma ta hanyar samar da isassun kayan aiki da tallafi ga hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."
"Ina son na godewa bankin duniya bisa goyon bayan da yake ba wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da burin bankin na rage fatara da inganta ci gaba mai ɗorewa."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Lawal ya kuma tabbatar wa jami’an bankin duniya cewa gwamnati za ta samar da cikakken tsaro a duk lokacin da suke zuwa jihar don bayar da tallafi, sa ido ko kuma gudanar da wasu ayyuka.

Gwamna Dauda ya yi alhinin rasuwar Almajirai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nuna alhininsa kan gobarar da ta ritsa da wasu Almajirai a wata makarantar allo da ke Kauran Namoda.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

Gwamna Dauda Lawal ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar almajiran inda ya yi alƙawarin gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng