Dakarun Sojoji Sun Yi Taron Dangi kan 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Miyagu Masu Yawa

Dakarun Sojoji Sun Yi Taron Dangi kan 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Miyagu Masu Yawa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun ƙara nuna ƙwazo da jajircewa a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 44 a farmakin haɗin gwiwa da suka kai a sansanoninsu da ke jihar
  • Jami'an tsaron a yayin farmakin, sun raunata ƴan ta'addan masu tare da fatattakarsu daga wuraren da suke samun mafaka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 44 tare da jikkata wasu guda 25 a hare-haren haɗin gwiwa da suka kai a jihar Zamfara.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Zamfara
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Zamfara Hoto: @ZazagolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa dakarun sojojin na rundunar Operation fansan Yamma ne suka kai farmakin wanda aka yi wa laƙabi da Tsaftar Daji III.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya fadi nasarorin da aka samu kan 'yan bindiga a jihar

Jami'an tsaron sun fara farmakin ne a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2025, inda sojoji suka kai hari a maɓoyar ƴan ta’adda da ke yankin Mashema, wanda ya yi ƙaurin suna wajen zama sansanin ƴan bindiga da ƴan ta’adda.

Dakarun na rundunar musamman ta Birged 1, tare da haɗin gwiwar ɓangaren sojojin sama na Operation Fansan Yamma ne suka jagoranci kai farmakin.

Yadda farmakin ya gudana

Farmakin ya fara ne da ƙarfe 08:00 na safe, inda rukuni na farko ya kutsa kai cikin sansanonin ƴan ta’adda, sannan suka fatattake su daga Kashabawa, Bwarare, da Zaki, kafin su isa tsaunin Sakarawa.

Da isarsu tsaunin, sojoji sun fuskanci turjiya daga ƴan ta’adda waɗanda suka kafa sansani mai ƙarfi a kan dutsen.

Majiyoyin sirri sun nuna cewa ƴan ta’adda sun binne bama-bamai a hanyar shiga sansaninsu.

Sakamakon hakan sai sojoji suka yi amfani da dabarar kai farmaki daga gefe don gujewa tarkon bama-bamai.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun nuna kwarewa, sun yi ajalin tantiran 'yan bindiga

A lokaci guda, sojojin ƙasa da jiragen yaƙi na OPFY sun kai farmaki mai ƙarfi a sansanin ƴan ta’addan, inda suka yi masu mummunar ɓarna.

Duk da nasarar fatattakar ƴan ta’addan, dakarun ba su samu damar karɓe dutsen gaba ɗaya ba saboda yawan bama-baman da aka binne a ƙasansa.

Saboda haka, jirgin yaƙin ya sake dawowa domin ƙarin luguden wuta daga sama, inda ya hallaka ƙarin ƴan ta’adda da dama.

A wani farmaki na daban, sojojin da ke ci gaba da matsawa zuwa Badarawa sun fuskanci turjiya daga wajen ƴan ta’adda, amma daga baya sun samu nasarar fatattakar su daga wasu sansanoninsu.

Daga cikin ƴan ta’adda 44 da aka kashe, akwai wasu manyan kwamandoji da ake alaƙanta su da shahararrun tantiran ƴan bindiga, Bello Turji da Sani Black.

Kwamandojin ƴan ta'addan da aka hallaka sun haɗa da, Sanni Bammuwa, Kachallah Auta (wanda ya kasance mataimakin Sani Black), Audu Gajere, Kabiru Jangeru da Dan-Kane (ɗan Audu Jabbi)

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Zamfara

Ba a samu asara ba daga ɓangaren sojoji

Duk da fafatawar da aka yi da fuskantar barazanar bama-bamai, ba sojan da ya rasa ransa a wannan farmakin.

Wannan nasara wata babbar alama ce cewa sojojin Najeriya na ci gaba da samun galaba kan ƴan ta’adda a Zamfara, tare da ƙarfafa matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 27 a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar cafke wasu ƴan ta'addan tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng