Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'adda a Jihar Zamfara

Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'adda a Jihar Zamfara

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a jihar Zamfara
  • Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda tare da jikkata wasu da dama a wani samame da suka kai musu a maɓoyarsu da ke tsakanin Zurmi da Shinkafi
  • Jami'an tsaron sun kuma ƙwace ikon wani tsauni wanda ƴan ta'adda suke amfani da suke amfani da shi wajen yi wa sojoji kwanton ɓauna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation fansan Yamma, sun samu nasara kan ƴan ta'adda a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun hallaka aƙalla ƴan ta'adda guda 50 a wani samame da suka kai musu a jihar Zamfara.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Zamfara
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a jihar Zamfara. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka kashe 'yan ta'adda 27 tare da kwato makamai masu tarin yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda

A farmakin wanda aka yi wa taken fansar ƴan bindiga, dakarun sojojin sun kashe miyagu sama da 50 tare da jikkata aƙalla 25, ciki har da manyan kwamandojin ƴan ta’adda da ke biyayya ga Bello Turji da Sani Mai Nasara (Sani Black).

Daga cikin manyan ƴan ta’adda da aka kashe akwai: Kachallah Sanni Bammuwa, Kachallah Auta, Audu Gajere, Kabiru Jangeru.

Sannan akwai Dan-Gajere (ɗan Audu Jabbi) da Bako Mala’ika wanda ya addabi yankin Tungan Dan Musa.

Wannan farmaki shi ne karo na farko cikin shekaru da sojoji suka samu damar kutsawa da mamaye tsaunin Tungan Fulani, wurin da ya kasance mafakar ƴan ta’adda a tsakanin Zurmi da Shinkafi.

Rahotanni sun nuna cewa sojoji sun yi ƙoƙarin kutsawa yankin har sau biyar a baya amma duk ba su yi nasara ba, saboda ƴan ta’adda da kuma asarar rayuka da kayan yaki da sojoji suka fuskanta.

Kara karanta wannan

Dabara ta fara ƙarewa ƙasurgumin ɗan bindiga, sojoji sun koma maɓoyar Bello Turji

Dakarun sojoji sun samu galaba

An fara jin tsoron wurin ne tun bayan wani kwanton ɓauna da aka yi wa sojoji a 2019, lokacin da Bello Turji da Sani Black suka kashe wani babban soja (Manjo) da sojoji 16 da ke tafiya zuwa garin Mashema.

Bayan wannan harin, sojoji sun janye daga yankin, wanda hakan ya bai wa ƴan ta’adda damar karɓe ikon yankin.

Haka nan, a ranar 30 ga watan Agusta, 2024, mayaƙan Bello Turji da Sani Black sun sake kai wani farmaki a ƙauyen Kwashebawa, inda suka ƙona motar yaƙi sannan suka kashe sojoji biyu.

Wani babban jami’in soja ya bayyana cewa:

"Lokacin ɓoyewa ya ƙare. Dole ne Bello Turji, Sani Black, da mayaƙansu su miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba, ko kuma su baƙunci lahira."
"Ba za a sake yin wata yarjejeniya ko ba su wata ƙofa ba. Idan ba su miƙa wuya ba, za su fuskanci fushin hukuma."

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi galaba a kan manyan 'yan ta'adda a Zamfara

Muhimmancin nasarar ƙwato tsaunin Tungan Fulani

Tsaunin Tungan Fulani na da muhimmanci sosai ga ƴan ta’adda, domin ya zama wata hanya da ake amfani da ita wajen safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar da Mali.

Rahotanni sun nuna cewa Bello Turji da Sani Black sun daɗe suna ajiyar makamai, shirya hare-hare, da kuma sace mutane domin neman kuɗin fansa a wannan wurin.

Ƙwace wurin da sojoji suka yi na nufin an daƙile hanyar samun makaman ƴan ta’adda. Sannan an katse hanyarsu ta tserewa zuwa dazukan da ke kusa.

Sojoji sun kashe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji masu aikin samar da zaman lafiya sun samu nasara kan ƴan ta'adda a sassan daban-daban na Najeriya.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 27 tare da ƙwato makamai masu tarin yawa daga hannunsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng