Yan Bindiga Sun Tare Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Fasinjoji zuwa Daji

Yan Bindiga Sun Tare Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Fasinjoji zuwa Daji

  • Miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tafka aika-aika a jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Ana zargin yan bindigan sun yi wa wasu matafiya kwanton ɓauna a kan titi, inda suka tursasu zuwa cikin ƙungurmin daji
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ba da tabbacin cewa jami'anta sun bazama cikin daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 10 a yankin Ipele, kan titin babbar hanyar Benin-Owo a jihar Ondo.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa fasinjojin na cikin tafiya ne lokacin da ƴan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna.

'Yan bindiga sun sace matafiya a Ondo
'Yan bindiga sun sace fasjnjoji a jihar Ondo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa motar da aka sace fasinjojin a cikinta, ta wani kamfanin sufuri ne da ya yi suna.

Kara karanta wannan

"Zargin baki biyu": Fusatattun mutane sun bankawa gidan basarake wuta a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun sace fasinjoji

Ƴan bindigan sun bar motar a bakin titi, yayin da aka tursasa fasinjojin shiga cikin daji.

Wani direba da ya tsira daga harin ya shaidawa manema labarai a birnin Akure, a ranar Talata cewa lamarin ya faru ne a ƙarshen mako, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Fasinjojin sun fito ne daga yankin Kudu maso Gabas lokacin da ƴan bindigan suka far musu, sannan suka tafi da mutum 10 daga cikinsu."

- Wani direba

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da lamarin

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da sace mutanen a ranar Talata.

Sai dai kakakin ƴan sandan, ta ce mutum bakwai aka sace, ba mutum 10 ba, kuma jami’an tsaro sun bazama cikin dajin domin ceto su.

"Abin da muke da tabbaci a kai shi ne mutum bakwai aka sace. Jami’anmu tare da sauran hukumomin tsaro sun fara aiki don ganin an ceto mutanen da aka sace."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki

- Funmilayo Odunlami-Omisanya

Wannan sabon harin dai ya biyo bayan ƙorafin da mazauna garin Upenmen, a ƙaramar hukumar Owo, suka yi a kwanakin baya kan yawaitar hare-hare da sace mutane da ƴan bindiga ke yi a yankin.

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da muggana makamai sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Lau ta jihar Taraba.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da wasu mutum tara bayan kwashe lokaci suna harbe-harbe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng