Yan Bindiga Sun Shiga Gari Gari, Sun Kashe Bayin Allah duk da Gwamna Ya Yi Sulhu da Su
- Ƴan bindiga sun afkawa mutane a wasu kauyuka da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna ranar Litinin, sun kashe mutum nan take
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma jikkata wasu, sannan suka yi awon gaɓa da mutane biyar zuwa wurin da ba a sani ba
- Wani mazaunin yankin ya yi kira ga gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakan kare su daga sharrin waɗannan maharan da ba su da tausayi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Miyagun 'yan bindiga sun afkwa mutane a kauyen Kumana da ke yankin gundumar Kwassam da kuma Rumaya a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Ƴan bindigar sun kai wannan mummunan hari ne a daidai lokacin da gwamnatin Kaduna ke ikirarin an samu zaman lafiya sakamakon sulhu da ƴan ta'adda.

Asali: Twitter
Jaridar Leadership ta tattaro cewa maharan sun kashe mutum biyu tare da sace wasu mutane biyar a sabon harin da suka kai kauyukan ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun shiga gari-gari a Kaduna
Haka nan, wasu mutane uku sun sami raunuka daban-daban sakamakon harbin bindiga da maharan suka yi a harin na ranar Litinin, wanda ya bar mazauna yankin cikin tsoro da firgici.
Maharan, waɗanda suka shiga cikin garuruwan da yawansu, sun buɗe wuta ba kakkautawa a harin, lamarin da ya jefa jama’a cikin tashin hankali.
Wani mazaunin T/Wada Garmadi, Mista Joel Ahada, ya tabbatar da faruwar harin tare da yin Allah-wadai da wannan aika-aika.
Ya bayyana harin a matsayin rashin mutunta haƙƙin dan Adam da kuma barazana ga tsaron mazauna yankunan karkara, rahoton Daily Trust.
An buƙaci gwamnati ya ɗauki matakin gaggawa
Ahada ya koka da cewa:
“Ko gwamnatinmu ta rufe kunnuwa kan halin da muke ciki ne? Muna buƙatar daukar matakin gaggawa da kuma kare rayukanmu."
Ya bayyana sunayen waɗanda suka rasa rayukansu da Shehu Umaru da Philip Barde, yayin da waɗanda suka ji raunuka suka hada da Vincent Danjuma, Francis Habila, da Amu Bawa.
Bugu da ƙari, Ahada ya faɗi sunayen waɗanda aka sace da suka hada da Shekarau Umaru, Nathan Danjuma, Augustine Samuel, Dawo Bawa, da Hon. Christopher Sayi.
Ya yi kira da a yi addu’a domin samun rahamar waɗanda suka rasu, da kuma fatan Allah ya kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su tare da baiwa waɗanda suka ji raunuka sauƙi cikin gaggawa.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai samu nasara ba har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto.
Jami'an tsaro sun ceto mutanen da aka sace
A wani labarin, kun ji cewa dakarun ƴan sanda da sojoji sun gwabza da ƴan bindiga, sun ƙwato mutane 23 da aka yi garkuwa da su a Kaduna.
An ruwaito cewa jami'an tsaron sun farmaki ƴan ta'addan bayan samun bayanan sirri a yankin karamar hukumar Kauru, inda suka yi nasarar kuɓutar da mutanen lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng