'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da 'Yan Mata a Wani Mummunan Hari

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da 'Yan Mata a Wani Mummunan Hari

  • Ƴan bindiga sun yi ta'asa a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Neja da ke fama da matsalar rashin tsaro
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka ɗan banga mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu ƴan mata guda shida
  • Mazauna yankin Pandogari sun koka kan yadda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka bayan an yi sulhu da su a Kaduna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ƴan mata shida a jihar Neja.

Ƴan bindigan sun sace ƴan matan ne masu shekaru tsakanin 15 da 17 a yankin Pandogari da ke ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja.

'Yan bindiga sun kai hari a Neja
'Yan sun sace 'yan mata a jihar Neja Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Laraba da daddare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a kauyen Neja

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a daren Juma'a, mutanen gari sun masu tara tara, an rasa rai

Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka wani ɗan banga mai suna Aliyu Aminu kafin daga bisani suka sace ƴan matan.

A cewar mazauna yankin, ƴan bindigan sun shigo garin ne ta yankin Birnin Gwari, ta hanyar kwalejin Mamman Kontagora da ke Pandogari.

Majiyoyi sun ce ƴan bindigan sun tafi da ƴan matan da aka sace ne zuwa dajin Kwangel.

Wata majiya ta ce ƴan bindigan sun riƙa shiga gidaje ɗaya bayan ɗaya a lokacin harin da suka kai da daddare.

"Harin da aka kai a daren Laraba shi ne karo na uku a cikin mako guda. Sun fara kai mana hare-hare tun bayan sulhun da suka yi da gwamnatin jihar Kaduna."
"Wannan sulhu da aka yi da su da mazauna Birnin Gwari bai amfanemu da komai."
"Tun daga lokacin da gwamnatin Kaduna ta yi sulhu da su a Birnin Gwari, sai suka dawo kai hare-hare a nan."
"A makon da ya gabata, sun zo sun sace mutane ciki har da hakimin garin. Sun zo sau biyu kafin harin da suka kawo a daren ranar Laraba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

- Wata majiya

Shugaban ƙaramar hukuma ya yi bayani

Shugaban ƙaramar hukumar Rafi, Ayuba Usman Katako, ya tabbatar da harin, inda ya ce gwamnatocin jihohin Neja da Kaduna dole ne su haɗa kai domin tabbatar da tsaron jihohin biyu.

"Gaskiya ne cewa ƴan bindiga sun kai hari a yankin Pandogari. A haƙiƙanin gaskiya, ba wannan ne kawai harin da suka kai a cikin makonni biyu da suka gabata. Harin da suka kai a ranar Laraba shi ne karo na uku."
"A hare-haren da suka kai a baya, sun yi nasarar sace wasu mutane a wasu ƙauyuka, amma a ranar Laraba, sun kashe mutum ɗaya kafin su sace mutane takwas. Sai dai daga baya mutane huɗu daga cikinsu sun tsere."

- Ayuba Usman Katako

Ƴan bindiga sun sace fasinjoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun yi wa matafiya kwanton ɓauna a jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'adi, an gano gawar ɗan Majalisar da suka sace a wani yanayi

Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da mugayen makamai sun yi awon gaba da fasinjoji guda 10 zuwa cikin daji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng