'Ka Taka Masa Birki': An Kai Karar El Rufai gaban Ribadu, an Hango Hatsarin Kalamansa
- Kungiyar kare dimukradiyya, TAN ta bukaci Nuhu Ribadu da ya dakatar da Nasir El-Rufai kan wasu kalamai da take ganin suna da hadarin tayar da fitina
- El-Rufai ya soki gwamnatin Bola Tinubu yana kwatanta ta da mulkin soja, tare da zargin Gwamna Uba Sani da karɓar kudi daga Gwamnatin Tarayya a asirce
- TAN ta yi gargadin cewa irin wadannan kalamai na iya haddasa rikici a Kaduna da ma Arewa baki daya, don haka dole ne a dauki matakin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kaduna - Kungiyar kare dimokuradiyya ta Transparency and Accountability Network (TAN), ta kai karar Nasir El-Rufai ga Nuhu Ribadu.
Kungiyar ta bukaci mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ya taka wa tsohon gwamnan Kaduna birki kan wasu kalamansa.

Asali: Facebook
Kungiya ta zargi El-Rufai da neman rigima
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a a Abuja, TAN ta ce dole ne ta yi magana kan wannan batu mai matukar muhimmanci, saboda yana barazana ga zaman lafiya, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TAN tana fargabar cewa kalaman El-Rufai za su iya zama matsala ga zaman lafiyar Arewa da Kaduna
Baya ga zargin Gwamna Uba Sani da karɓar biliyoyin nairori daga Gwamnatin Tarayya ba tare da bayyanawa al’umma ba, El-Rufai ya kwatanta gwamnatin Tinubu da mulkin soja.
"Waɗanda suka rayu a ƙarƙashin mulkin soja sun san menene ba, Ba mu son mulkin soja, kuma ba mu son fararen hula suna yin mulkin soja a cikin babbar riga.
"Idan ba a yi gaggawar magance wannan batu ba, yana iya yaduwa zuwa wasu sassan Arewa da ma ƙasa baki daya.
- Cewar sanarwar
Shugaban TAN, Michael Briggs, ya ce irin waɗannan kalamai dole ne a dakatar da su nan take, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara
TAN ta ce kalaman El-Rufai na nuni da wata manufa ta ɓoye, wacce ka iya haddasa rarrabuwar kai da rikici a jihar Kaduna.
TAN ta kai karar Nasir El-Rufai ga Nuhu Ribadu
“Ba jita-jita ba ne kawai; jita-jitar tana ƙara ƙarfafa kalamansa na baya-bayan nan, inda ya shawarci ‘yan adawa da su shirya tsaf domin kalubalantar jam’iyyarsa, APC, a 2027.”
"Kaduna jiha ce da aka fi sani da hadin kai da ci gaba, amma ta sha fama da rikici, jama’an jihar sun sha wahala, sun yi jini, sun yi hawaye, kuma sun shiga cikin bakin ciki.
- Kungiyar ta ba da tabbaci
TAN ta ce dole ne hadimin ya dauki matakin gaggawa kan El-Rufai kamar yadda mai kashe gobara ke hanzarin kashe wuta kafin ta bazu.
Naja'atu: El-Rufai ya yi tone-tone kan Ribadu
Kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya goyi bayan kalaman Naja’atu Muhammad kan zargin Nuhu Ribadu ya taba sukar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Matasan Arewa sun fadi sunayen 'yan siyasa 3 da ke shirin ruguza gwamnatin Tinubu
Nuhu Ribadu ya musanta zargin, yana mai cewa ba zai lamunci bata masa suna ba tare da bukatar Naja’atu ta ba da hujjoji ko a ba shi hakuri kafin a je kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng