Bidiyon Naja'atu: Ribadu Ya Dauki Zafi, Ya ba 'Yar Gwagwarmayar Wa'adi kan Bata Suna
- Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci Naja’atu Muhammad ta janye kalamanta a bidiyon TikTok da ta yi
- A cikin bidiyon, Hajiya Naja’atu ta zargi Ribadu da goyon bayan gwamnatin Tinubu, wanda a baya ya soka a lokacin da yake shugaban EFCC
- Lauyan Ribadu ya ce ya kamata Hajiya Naja’atu ta janye maganganunta kuma ta bayar da hakuri a jaridu guda biyar cikin kwanaki bakwai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mai ba da shawara kan tsaro na kasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bukaci Hajiya Naja’atu Muhammad ta nemi afuwa kan bidiyon da ya yi.
Nuhu Ribadu ya bukaci ta janye kalamanta a wani bidiyon TikTok da ya ce ta yi ne domin bata masa suna.

Kara karanta wannan
"A ajiye duk manufar da za ta wahalar da talaka," Gwamna ya soki tsare tsaren Tinubu

Asali: Twitter
Tinubu: Hajiya Naja'atu Muhammad ta soki Ribadu
A cikin wata wasika ta hannun lauyansa, Dr. Ahmed Raji, SAN, NSA ya ce ko a fili ko a asirce, bai taba fadin irin wannan ra’ayi ba, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Hajiya Muhammad ta zargi hadimin da yin aiki a gwamnatin Bola Tinubu, wanda a baya ya soka lokacin da yake shugaban hukumar EFCC.
Ya ce barnar da aka yi sakamakon wannan bidiyon TikTok ba za a iya auna ta ba.
"A cikin wasikar ranar 4 ga Fabrairu, 2025, Dr. Raji ya ce Hajia Naja’atu ta bayyana cewa NSA ya taba zargin Tinubu da wasu gwamnoni da satar kudi.
"Har ila yau, ta ce yanzu NSA ya zama mai kare Tinubu, musamman dangane da manufar gwamnati na hana mutane su soki gwamnati.
"Ta kuma ce canjin matsayin NSA yana nufin ko dai ya kasance makaryaci ne ko kuwa ya yi karya lokacin da ya soki wadancan shugabanni."
- Cewar sanarwar
Nuhu Ribadu ya musanta zargin Naja'atu
Nuhu Ribadu ya musanta cewa ya taba fadin irin wadannan zarge-zarge kan Tinubu, Akume da Kalu, yana mai cewa abin ya zo masa da mamaki.
Ya bukaci Hajia Naja’atu da ta kawo hujjoji kan abin da ta fada game da shi, domin kalamanta sun bata masa suna.
Ya ce bidiyon nata yana da hadarin tayar da fitina a Arewa, kuma ba zai yi shiru a kan hakan ba.
Lauyan ya ce Hajia Naja’atu ta wallafa wannan bidiyon da nufin bata masa suna tare da janyo duniya ta zarge shi.
Ya ce hadimin ba zai bari a bata sunansa haka kawai ba, kuma dole ne a cire bidiyon tare da bada hakuri a jaridu guda biyar.
Idan ba a yi hakan cikin kwanaki bakwai ba, Ribadu zai dauki matakin shari’a don neman diyya a kotu.
Ribadu ya magantu kan matsalar tsaro

Kara karanta wannan
"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'
A wani labarin, Mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya fadi matakan da ya kamata a dauka kan rashin da tsaro.
Ribadu ya ce yaki da ta'addanci ba zai yi nasara ba sai da hadin kan al'umma da gaggawar bayar da rahoto kan duk abin da ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng